Yadda hadiman Buhari suka bata masa suna, suka mayar da Nigeria abar dari, Dan majalisa ya bayyana

Yadda hadiman Buhari suka bata masa suna, suka mayar da Nigeria abar dari, Dan majalisa ya bayyana

- Dan majalisa, Laori Kwamoti, ya ce hadiman Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun mayar da Najeriya abun dariya

- Kwamoti ya ce rashin kwarewar hadiman Buhari ya bata ma Shugaban kasar suna da mutuncinsa

- Dan majalisan ya yi gargadin cewa Najeriya ba za ta ci gaba ba har sai an dauki kwararru don kula da Shugaban kasar da gwamnatinsa

Laori Kwamoti, wani dan majalisan Adamawa mai wakiltan mazabar Numan/Lamurde/Demsa a majalisar wakilai, ya koka kan yadda hadiman Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke bata masa suna.

Dan majalisan ya bayyana matsayarsa a ranar Talata, 12 ga watan Janairu, a garin Yola, inda ya kara da cewa hadiman Shugaban kasar sun yi barna sosai a gwamnatinsa.

A cewarsa, furuci mara ma’ana da martanin mafi akasarin masu kula da harkokin labaran Shugaban kasar ya “rage darajar Najeriya zuwa abar dariya.”

Yadda hadiman Buhari suka bata masa suna, suka mayar da Nigeria abar dari, Dan majalisa ya bayyana
Yadda hadiman Buhari suka bata masa suna, suka mayar da Nigeria abar dari, Dan majalisa ya bayyana Hoto: @Kwamoti
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Jerin sunaye: Hukumar yan sandan Najeriya ta sanar da sabbin nade-nade

Kwamoti, wanda ya kuma bayyana cewa Najeriya na daukar wasu mutane da hukumomi a matsayin wadanda suka fi karfin doka, ya yi gargadin cewa kasar za ta ci gaba da komawa baya idan aka ci gaba da mulkin kama karya, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Ya kara da cewa kada yan Najeriya su yi tsammanin kowani sauyi mai kyau daga gwamnati mai ci har sai Buhari ya kawo mutane masu mutunci da tunani.

“Ku duba wannan batu; Shugaban kasar ya fada ma duniya cewa zai gurfana a gaban majalisar dokokin tarayya, kawai sai ga wasu hadimai marasa kwarewa sun fito suna fadin cewa mu (yan majalisar tarayya) bamu da ikon gayyatar Shugaban kasar. Shin wannan ba abun kunya bane?

“A kasar daa mutane suka fi karfin kotuna, yan sanda, sojoji da sauran hukumomin da sune ginshikin damokradiyya babu inda za a je; za ta ci gaba da kasancewa koma baya.”

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya amince da nadin jakadu 95

A wani labarin kuma, Shugaban cocin Living Christ Mission Incorporated, Daddy Hezekiah, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta daina cin bashi daga kasar China.

Farfesa Daddy Hezekiah wanda shi ne wanda ya kafa jami’ar Daddy Hezekiah da ke jihar Imo, ya ce cin bashi musamman daga Sin yana da matukar hadari.

Jaridar Vanguard ta rahoto Daddy Hezekiah ya na sukar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke rabon mukaman mukarraban na kusa da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng