Shugaba Buhari ya amince da nadin jakadu 95
- Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin jakadu 95 zuwa kasashe daban-daban
- Gwamnatin tarayya ta bayyana hakan a ranar Talata, 12 ga watan Janairu
- Sai dai babu wani cikakken bayani a kan wadanda za a nada kan wannan matsayin
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a tura jakadun Najeriya 95 zuwa kasashe daban daban.
Hakan ya biyo bayan samun amincewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari game da nadin jakadun, Channels TV ta ruwaito.
Ma’aikatan harkokin waje ta bayyana hakan a cikin wani jawabi a ranar Talata, 12 ga watan Janairu, daga sakataren dindindin na ma’aikatar, Ambassador Gabriel Aduda.
KU KARANTA KUMA: Dan kasuwa ya sayi wayoyin iPhone har na N45m amma babu komai a kwalayen
Yayinda Aduda bai bayyana lokacin da Shugaban kasar ya bayar don amincewa da nadin ba, ya bayyana cewa wadanda za a tura sun hada da jakadu 95.
Sakataren na dindindin ya bayyana cewa ma’aikatar za ta shirya wani taro na wayar da kai ga jakadun da matayensu.
Ya yi bayanin cewa taron wanda za a gudanar a ranar da za a sanar a nan gaba kadan zai kasance don shiryawa da sanar da jakadun ayyukan da za su gudanar.
KU KARANTA KUMA: Gaba da kowa: Jami'ar ABU Zaria za ta buɗe makaranta 25 ga Janairu
A wani labari na daban, Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattijai, ya ce bai zama shugaban majalisar dattijai a shekarar 2015 ba saboda ba'a lokacin Allah ya tsara zai hau kujerar ba.
Sanata Lawan ya bayyana hakan ne yayin wani taron ta ya shi murnar cika shekaru 62 da aka shirya a Abuja, kamar yadda TheCable ta rawaito.
Da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai, Lawan ya ce duk da bai samu nasara a wancan lokacin ba, hakan bai hana shi yin aiki hannu da hannu da Bukola Saraki ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng