Daddy Hezekiah: Karbo aron kudin da Gwamnati ta ke yi daga Sin yana da hadari

Daddy Hezekiah: Karbo aron kudin da Gwamnati ta ke yi daga Sin yana da hadari

- Shugaban cocin Living Christ Mission Incorporated ya soki Gwamnatin APC

- Daddy Hezekiah ya ce karbo bashi daga hannun Gwamnatin Sin ya na da illa

- Faston ya ce an murde zaben Amurka, ya yi kira ayi wa Donald Trump addua

Shugaban cocin Living Christ Mission Incorporated, Daddy Hezekiah, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta daina cin bashi daga kasar China.

Farfesa Daddy Hezekiah wanda shi ne wanda ya kafa jami’ar Daddy Hezekiah da ke jihar Imo, ya ce cin bashi musamman daga Sin yana da matukar hadari.

Jaridar Vanguard ta rahoto Daddy Hezekiah ya na sukar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke rabon mukaman mukarraban na kusa da shi.

Faston yace muddin gwamnatin APC mai mulki ba ta canza salo na son kai wajen rabon kujeru ba, abubuwa ba za su dawo daidai a kasar nan ba.

KU KARANTA: Magoya baya suna so Gwamnan Kogi ya yi takarar shugaban kasa

“Gwamnatin APC a Najeriya ba ta da wata daraja, kuma mutane masu daraja ne kawai za su iya ceto Najeriya daga halin da ta ke ciki a dalilin jam’iyyar da ke mulki.”

A cewar Hezekiah, ana bukatar ayi wa tsarin Najeriya garambawul kafin a ci moriyar arzikin al’umma da albarkatun da kasar ta ke da shi.

Da ya ke magana, Fasto Hezekiah ya tofa albarkacin bakinsa game da zaben kasar Amurka, ya ce an yi magudi a zaben 2020 wanda Donald Trump ya sha kasa.

Faston ya ce zaben abin kunya ne ga kasar Amurka da ta zama abin koyi ga Duniya. Hezekiah ya ce nasarar Joe Biden hadari ne saboda goyon bayan auren jinsi.

KU KARANTA: Fadar Shugaban ta fadi dalilin da ya sa aka fama da matsalar tsaro

Daddy Hezekiah: Karbo aron kudin da Gwamnati ta ke yi daga Sin yana da hadari
Daddy Hezekiah (MFR, JP) Hoto: www.cib.com.ng
Asali: UGC

Farfesan ya yi kira ga kiristoci su yi wa Donald Trump addua’a, ya soki tafiyar tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama da manufofinsa na 'shaidanci'.

A zaben 2023, babban jigon APC a kasar Ibo, Sanata Rochas Okorocha ya fara kiran ‘Ya 'yan jam'iyyar PDP da APC su hada-kai domin a kawo gyara a Najeriya.

Rochas Okorocha ya ce akwai bata-gari a dukannin jam'iyyun na PDP da APC, don haka ya ke neman na kwaran da su ka rage su kawowa al'umma dauki.

Tsohon gwamna Rochas Okorocha ya bayyana haka ne da aka gayyace shi ya kaddamar da wasu tituna a Ribas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng