Dan kasuwa ya sayi wayoyin iPhone har na N45m amma babu komai a kwalayen

Dan kasuwa ya sayi wayoyin iPhone har na N45m amma babu komai a kwalayen

- Wani matashin dan kasuwa a kasar Ghana wanda ke siyar da kayyaki kirar APC ya tuna yadda yayi asarar N45m a wani ciniki

- A cewarsa, ya yi odan wayoyin iPhone 12, iPhone 12 Pro, da iPhone 12 pro max daga wani mai tura kayayyaki da yayi aiki dashi tsawon shekaru uku

- Ga mamakin dan kasuwan, dukka kwalayen da aka turo masa babu komai a ciki kuma ya gaza gano inda mai turo kayan ya shiga

Wani matashi dan kasuwa daga kasar Ghana wanda ke gudanar da kamfanin IgoodsghGhana Limited ya bayyana cewa a 2020, ya yi asarar kudi kimanin N45m sanadiyar aminta da yayi da wani mai tura kaya.

A wani wallafa a shafinsa na Twitter, dan kasuwan ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a 2020 lokacin da yayi odan kayayyakinsa sannan aka kawo masa kwalayen ba komai ciki.

KU KARANTA KUMA: Gaba da kowa: Jami'ar ABU Zaria za ta buɗe makaranta 25 ga Janairu

Dan kasuwa ya sayi wayoyin iPhone har na N45m amma babu komai a kwalayen
Dan kasuwa ya sayi wayoyin iPhone har na N45m amma babu komai a kwalayen Hoto: @igoodsghana
Asali: Twitter

A cewarsa, kayayyakin da yayi oda sune waya iPhone 12, 12 Pro, da 12 Pro max amma sai aka kawo masa kwalaye babu komai a cikinsu bayan ya biya kudaden su.

Kalli wallafar a kasa:

Abunda zai baka al’ajabi, ya dade yana harka da mai turo kayan kusan kimanin shekaru uku amma duk wani kokari da aka yi don gano shi bai cimma nasara ba.

Matashin dan kasuwan ya ci gaba da bayanin cewa ya kwashe tsawon shekaru tara yana kasuwancin kuma ya hadu da masifa da dama amma duk da haka yana ci gaba da harkokinsa.

KU KARANTA KUMA: Na koma APC ne domin na gina rayuwar ‘ya’yana, In ji Sanata Abbo

A wani labarin, kungiyar maza masu rowa da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng