Ma'aikatan jami'a zasu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani ranar a Alhamis

Ma'aikatan jami'a zasu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani ranar a Alhamis

- Gamayyar kungiyoyi uku na ma'aikatan jami'a sun shirya tafiya yajin aiki idan aka gaza cimma bukatun su kafin kwana uku

- Tuni sun tsunduma zanga zanga bisa rashin amincewa da ingancin tsarin IPPIS

- Shugaban kungiyar ya ce suna da yakinin gwamnati zata duba bukatar su saboda kar su kawo tsaiko a karatun yara

Ma'aikatan jami'a da basa koyarwa a ranar Talata, sun gudanar da zanga zangar kwana uku a kasa baki daya don mika bukatun su wanda yafi shafar tsarin albashi na IPPIS, rashin biyan mafi karancin albashi da sauran su, Daily Trust ta ruwaito.

Zanga zangar hadin gwiwa ne tsakanin kungiyar ma'aikatan jami'a marasa koyarwa da kuma kungiyar manyan malaman jami'a wanda suka kaddamar a harabar jami'ar Abuja.

Ma'aikatan jami'a zasu tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani ranar Alhamis
Ma'aikatan jami'a zasu tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani ranar Alhamis. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bayan Nigeria, an bude kungiyar samari masu 'dunƙule hannu' a kasashe 5

Shugaban kungiyar SSANU, Mohamed Ibrahim, wanda ya jagoranci zanga zangar ya ce za su dauki mataki na gaba ranar Alhamis idan gwamnati bata duba bukatun su, ya ce zanga zangar kawai dan jan kunne ne.

"Idan gwamnati ta ci gaba da gardama kuma bata duba bukatar ba, JAC za su dauki mataki na gaba ranar Alhamis. Muma akwai yayan mu a jami'a. Mu a fatan mu, muna fata kuma muna sa rai gwamnati zata yi abin da ake bukata kafin mu kare zanga zangar kwana ukun, amma idan anki, wanda ba ma fatan haka ;zamu sanar da duniya mataki na gaba'', a cewar shugaban kungiyar.

Anata bangaren, ma'ajin kungiyar NASU, Malama Sadiat Hassan, ta ce kungiyar baza yi wata wata ba wajen dakatar da al'amuran karatu a makarantu da dama ba idan gwamnati ta gaza sauraren bukatun su.

KU KARANTA: Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa

A cewar ta, "muna zanga zanga ne saboda rashin gamsuwa da tsarin biyan albashin IPPIS da kuma bukatar a sake duba yarjejeniyar da muka yi tun 2009 wanda tuni aka watsar.

"Muna zanga zanga ne bisa kin biyan mu hakkokin mu da rashin adalci da gwamnatin tarayya ke yi wajen raba kasafi saboda tana baiwa wata kungiya kaso 75 kungiyar su kuma kaso 25.

" Wannan ya sabawa yarjejeniyar da muka kulla cewa kudin na duka kungiyoyi ne. To, muna so ayi wa kowa adalci saboda wannan hakkin mu ne".

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel