Ahmed Lawan: Dalilin da yasa na sha kaye wurin Saraki a 2015
- An fafata takarar neman kujerar shugaban majaisar dattijai tsakanin Sanata Bukola Saraki da Sanata Ahmed Lawan a shekarar 2015
- Ahmed Lawan da Femo Gbajabiamila sun samu goyon bayan fadar shugaba kasa da uwar jam'iyyar APC a shekarar 2015
- Sai dai, duk da goyon da suke da shi a wancan lokacin, Ahmed Lawan da Gbajabiamila sun sha kaye hannun Saraki da Dogara
Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattijai, ya ce bai zama shugaban majalisar dattijai a shekarar 2015 ba saboda ba'a lokacin Allah ya tsara zai hau kujerar ba.
Sanata Lawan ya bayyana hakan ne yayin wani taron ta ya shi murnar cika shekaru 62 da aka shirya a Abuja, kamar yadda TheCable ta rawaito.
Da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai, Lawan ya ce duk da bai samu nasara a wancan lokacin ba, hakan bai hana shi yin aiki hannu da hannu da Bukola Saraki ba.
Jam'iyyar APC mai mulki ta zabi Lawan da Gbajabiamila a matsayin 'yan takarar ta na shugaban majalisar dattijai da majalisar wakilai a shekarar 2015.
Sai dai, dukkansu sun sha kaye a hannun 'yan takarar da basu da goyon bayan uwar jam'iyya da fadar shugaban kasa.
Bukola Saraki ya lashe zaben kujerar shugaban majalisar dattijai a yayin da Yakubu Dogara ya lashe zaben zama shugaban majalisar wakilai a 2015.
KARANTA: Shekau ya saki faifan sako na farko a cikin 2021, ya gargadi Sheikh Ahmad Gumi
Sai dai, an shiga 'yar tsama da zaman doya da manja a tsakanin tsofin shugannin majalisar da fadar shugaban kasa da kuma uwar jam'iyya.
"Idan Za ku iya tunawa na nemi kujerar shugaban majalisar dattijai a shekarar 2015, amma Allah cikin ikonsa bai kaddara zan sameta a wancan lokacin ba.
"Ba lokaci bane, Allah ya riga ya tsara cewa Sanata Saraki ne zai hau kujerar a lokacin.
"Mun yarda da Allah, shi yasa muka yi aiki tare da shugabancin majalisa don kawowa jama'a cigaba har zuwa shekarar 2019, lokacin da Allah ya yi zan yi samu kujerar," a cewar Lawan.
Legit.ng Hausa ta rawaito cewa mazauna Kaduna ta tsakiya sun gudanar da zanga-zangar nuna fushi tare da yin kiran a dawo da wakilinsu, Sanata Uba Sani.
Masu zanga-zangar sun zargi Sanata Uba Sani da gina ganuwar karfe a tsakaninsa da Jama'ar da suka zabe shi.
Bayan hakan, sun ce yanzu gaba daya ma an daina gani da jin duriyar Sanata Uba Sani a zauren majalisar dattijai.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng