'Yan bindiga sun kashe dan takarar kansila na PDP a Delta

'Yan bindiga sun kashe dan takarar kansila na PDP a Delta

- Yan bindiga sun halaka dan takarar kansila a jihar Delta

- 'Yan bindigan sun kuma sace wasu mutane biyu da ke tare da shi

- Rundunar 'yan sandan Jihar Delta ta tabbatar da afkuwar lamarin

'Yan bindiga sun kashe dan takarar kansila na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben da za a gudanar a ranar 6 ga watan Maris a Delta, Mista Elliot Ofa.

The Nation ta ruwaito cewa yan bindigan sun sace wasu mutane biyu tare da shi.

'Yan bindiga sun kashe dan takarar kansila na PDP
'Yan bindiga sun kashe dan takarar kansila na PDP. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa

Sai dai a tabbatar ko kashe shi na da alaka da siyasa ba sakamakon wasu na zargin cewa tun farko wasu basu so aka nada shi a jam'iyyar ta PDP.

An gano, cewa lamarin ya faru ne a layin Jesse/Oben kusa da iyakar jihohin Delta da Edo.

Rahotanni sun ce an sace marigayin da wasu mutane biyu a yayin da suke dawowa daga ofishin hukumar zabe mai zaman kanta na jihar, DSIEC, a Asaba yayin da yan bindigan suka tare motarsu suka harbe shi ya kuma mutu.

KU KARANTA: Mai garkuwa ya biya N1.5m don fansar kansa daga hannun 'yan bindiga da suka sace shi

Kafin rasuwarsa, marigayin shine tsohon kansilar muhalli na karamar hukumar Ethiope-West.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar, DSP, Onome Onovwakpoyeya ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Ta ce: "Sun ce a Jihar Edo abin ya faru, ba a Delta ba."

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel