Zaben 2023: Jigo a Arewa dan APC ya bukaci a baiwa dan kudu takara

Zaben 2023: Jigo a Arewa dan APC ya bukaci a baiwa dan kudu takara

- Wani jigo a jam'iyyar APC daga arewacin Najeriya ya sake magantuwa kan muhawarar takarar shugabancin kasa

- Sahabi Danladi Mahuta, jagoran APC a Jihar Kebbi, ya ce a mika wa yan kudu takara bayan shekara 8 dan arewa na mulki

- Mahuta, ya kuma ce dole ne musulmi dan arewa ya zama mataimaki saboda addini zai taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban siyasa

Sahabi Danladi Mahuta, wani babban jigo a jam'iyyar APC a jihar Kebbi kuma malamin addini, ya ce ya kyautu a bawa dan yankin kudu takarar shugabancin kasa a zaben 2023, jaridar ThisDay ta ruwaito.

Mahuta, ya kuma bayyana cewa in dai har an amince da bukatar baiwa dan kudu takara, to dole ne batun addini ya shigo ciki.

Zaben 2023: Jigo a Arewa dan APC ya bukaci a baiwa dan kudu takara
Zaben 2023: Jigo a Arewa dan APC ya bukaci a baiwa dan kudu takara. Hoto: Femi Adesina
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsohon shugaban majalisa, Joseph Wayas, yana kwance rai a hannun Allah a Landan

Jagoran na APC, saboda haka ya bayyana cewa a gabatar da kirista dan takara daga kudu, sai kuma mataimaki musulmi daga arewa.

Ya kuma yi bayanin cewa ko da musulmi dan kudu aka baiwa takara, arewa za su fi karkata kan baiwa musulmi takarar mataimakin.

Jigon ya kuma bayyana wasu yan siyasar kudancin Najeriya a matsayin wanda zasu iya maye gurbin shugaba Buhari a 2023.

KU KARANTA: 'Yan sandan Zamfara sun ki karbar toshiyar baki ta N250,000, sun kama ɓarawon mota

Su ne jagoran APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da kuma gwamnan Ekiti, Dr Kayode Fayemi.

Ya ce an san mutane biyun da jajircewa daga yankin kudu maso yamma kuma ana ganin su ne ke da yiwuwar yin takarar.

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164