Gwamnati za tayi zama na musamman a kan maganar komawa aji bayan kamarin COVID-19

Gwamnati za tayi zama na musamman a kan maganar komawa aji bayan kamarin COVID-19

- Ministan ilmi ya yi magana game da ranar da za a koma daukar darasi

- Adamu Adamu yace su na ta duba yiwuwar sake bude makarantun

- Za a fitar da sabuwar matsaya yau ganin yadda COVID-19 take yaduwa

A ranar Litinin, 11 ga watan Junairu, 2020, gwamnatin tarayya tace za ta duba maganar bude makarantu da ta sa cewa za ayi a ranar 1 ga watan nan.

Gwamnatin kasar ta ce hakan ya zama dole ne a sakamakon cutar COVID-19 da ta dawo da karfinta.

Jaridar Punch ta ce mai girma Ministan ilmi na kasa, Malam Adamu Adamu, ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida jiya a birnin Abuja.

Yace: “Bakin alkalami bai bushe game da batun bude makarantu a ranar 18 ga watan Junairu ba. Lokacin da muka sa wannan rana, muna harin abin da za mu yi aiki da shi ne kawai.”

KU KARANTA: Gwamatin Tarayya ta bada kwangilar dogo zuwa Nijar

Ministan ya ce suna burin cinma wannan matsayi da suka dauka, amma a daidai lokacin ana kuma duba halin da kasa ta ke ciki.

“Ko a ranar Litinin (wajen taron PTF), mun duba yadda alkaluma suke tashi, kuma mun yi maganar duba wannan rana da aka sa.” Inji Ministan.

Adamu Adamu ya tabbatar da cewa a ranar Talata ne ma’aikatarsa za ta zauna a kan maganar ranar komawa karatun domin a dauki matsaya.

Ganin yadda ake samun karuwar masu dauke da Coronavirs, Adamu Adamu ya nuna akwai matsala game da ranar da suka sa da nufin dalibai su koma aji.

KU KARANTA: Abin da ya sa mutane ba su yarda da COVID-19 ba

Gwamnati za tayi zama na musamman a kan maganar komawa aji bayan kamarin COVID-19
Ministan ilmi Adamu Adamu Hoto: www.ripplesnigeria.com
Source: UGC

Yau ne ake tunani ma’aikatar ilmi za ta bayyana ranar da za a koma shiga aji bayan an rufe makarantun saboda takaita yaduwar cutar COVID-19.

Dazu kun ji cewa NCDC ta fito ta ja-kunnen Jama’a bayan COVID-19 ta harbi mutane 100, 000.

Shugaban NCDC na kasa, Dr. Chikwe Ihekweazu ya ce cutar Coronavirus ta kai intaha a yanzu, ana gab da cike gadajen asibiti da masu jinya a Najeriya.

Dr. Chikwe Ihekweazu ya bayyana haka ne a wasu bayanai da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Litinin bayan masu cutar sun haura mutane 100, 000.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel