COVID-19: NCDC ta ce kwanan nan asibitoci za su rasa inda za su sa kansu

COVID-19: NCDC ta ce kwanan nan asibitoci za su rasa inda za su sa kansu

- Hukumar NCDC ta ce ana ta samun karuwar masu dauke da Coronavirus

- Chikwe Ihekweazu yace nan gaba asibitoci zasu rasa inda za su kai kansu

- A halin yanzu sama da mutum 100, 000 ne suka kamu da COVID-19 a kasar

Hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta ce Najeriya ta kai wani mataki mai kamari a yaki da ta ke yi da annobar Coronavirus.

Legit.ng ta samu labarin Darekta Janar na hukumar NCDC na kasa, Dr. Chikwe Ihekweazu ya na cewa asibitoci za su gagara sanin yadda za su yi da masu cutar.

Dr. Chikwe Ihekweazu ya bayyana haka ne a wasu bayanai da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

NCDC ta na magana game da yaduwar da cutar ta ke kara yi sosai, ta ce za a kai lokacin da ba a san inda za a kai wanda ciwonsu ya yi kamari ba.

KU KARANTA: Cutar korona ta kashe likitan Fafaroma

Shugaban NCDC ya ce nan gaba zai zamana babu isassun gadaje a asibitoci da za a kwantar da wadanda ciwon su ya yi nisa.

“Zai kai dole malaman lafiya za su dauki matakai masu tsauri. Muna bukatar mu kare wadanda suka shiga mawuyacin hali” Inji Ihekweazu

“Dole duk mu dauki dawainiya. Ba aikin NCDC, PTF ko gwamnati ba ne kawai. Idan ku na tara gangami, ku na jefa kanku da mutane ne a hadari.”

Dr. Ihekweazu ya gargadi jama’a cewa mutane 100, 000 da ake cewa sun kamu da COVID-19 a fadin kasar nan ba ta tatsuniya ba ne.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kyawun maganin COVID-19

COVID-19: NCDC ta ce kwanan nan asibitoci za su rasa inda za su kansu
Dr. Chikwe Ihekweazu Hoto: www.nature.com/articles
Asali: UGC

“A makonnni hudun da suka wuce, mun samu tashin gwauron-zabin masu COVID-19. Cutar tana yaduwa sosai.” NCDC tace hakan ya kai ga rasa rayuka.

Chikwe Ihekweazu ya bayyana wannan ne a daidai lokacin da jama’a suka koma wuraren rajistar shaidar zama ‘dan kasa bayan ma’aikata sun yi gajeren yajin-aiki.

Karamin Ministan lafiya na kasa, Dr. Olorunnimbe Mamora, ya shaidawa Channels Television cewa ana duba yiwuwar dakatar da rajistar NIN.

A gefe guda kuma kungiyar ASUU ta bayyana cewa bude makarantu a halin da ake ciki yana da matukar hadari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel