FG ta rattaba hannu kan kwangilar gina layin jirgin kasa daga Kano - Maradi da Kano - Dutse

FG ta rattaba hannu kan kwangilar gina layin jirgin kasa daga Kano - Maradi da Kano - Dutse

- Gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan kwangilar gina titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi da kuma daga Kano zuwa Dutse

- Minsitan sufuri, Rotimi Amaechi, ne ya saka hannu akan kwangilar da aka bawa wani kamfani mai suna Mota-Engil Group

- Kamfanin Mota-Engil Group ya dauki gina jami'a kafin ya kammala aikin a matsayin tukuicin aikin da zai yi a Nigeria

Gwamnatin tarayya, a ranar Litinin, 11 ga watan Janairu, 2021, ta rattaba hannu akan bayar da kwagilar gina titin jirgin kasa na zamani daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar da kuma daga Kano zuwa Dutse, babbn birnin jihar Jigawa.

Kamfanin da aka bawa kwangilar aikin, Mota-Engil Group, ya dauki alkawarin ginawa Nigeria Jami'a kyauta kafin kammala kwangilar da aka bashi.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ne ya sanar da hakan yayin da ya wallfa hotunansa yayin saka hannu akan kwangilar a shafinsa na dandalin sada zumunta.

KARANTA: Ahmed Musa ya sha nasiha da shawarwari bayan ya yada wani hotonsa da matarsa a dandalin sada zumunta

FG ta rattaba hannu kan kwangilar gina layin jirgin kasa daga Kano - Maradi da Kano - Dutse
FG ta rattaba hannu kan kwangilar gina layin jirgin kasa daga Kano - Maradi da Kano - Dutse @ChibuikeAmaechi
Asali: Twitter

A karshen shekarar 2020 ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da jiragen da zasu ke jigilar mutane a tsakanin Ibadan, jihar Oyo, da Legas.

KARANTA: Buhari ya bayar da dalilai hudu na kawo karshen Boko Haram a cikin shekarar nan

Fara sintirin jiragen a tsakanin Ibadan da Legas ya saka farinciki a zukatan 'yan Nigeria da ke harkokinsu a tsakanin jihohin biyu da kuma matafiya da ke shan azaba kafin shiga Legas saboda cunkuson ababen hawa.

A ranar Litinin ne Legit.ng ta rawaito cewa hukumar kula da harkar lafiya a matakin farko; NPHCD ta sanar da cewa nan bada dadewa za'a fara rabawa jihohi alluran rigakafi.

Gwamnatin tarayya ta ce zata yi la'akari da alkaluman masu kamuwa da cutar wajen rabon alluran rigakafin.

A cewar NPHCD, Jihar Kano za ta samu alluran rigakafi mafi yawa, 3,557, a rukunin farko na rabon.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: