Kaduna: Masu zabe sun yi zanga-zangar neman a dawo da Sanata Uba Sani, sun fadi dalili

Kaduna: Masu zabe sun yi zanga-zangar neman a dawo da Sanata Uba Sani, sun fadi dalili

- Mazauna Kaduna ta tsakiya sun gudanar da zanga-zangar nuna fushi tare da yin kiran a dawo da wakilinsu, Sanata Uba Sani

- Masu zanga-zangar sun zargi Sanata Uba Sani da gina ganuwar karfe a tsakaninsa da Jama'ar da suka zabe shi

- Bayan hakan, sun ce yanzu gaba daya ma an daina gani da jin duriyar Sanata Uba Sani a zauren majalisar dattijai

Dumbin mazauna Kaduna ta tsakiya sun gudanar da zanga-zangar lumana a tituna domin neman a dawo da wakiliansu a majalisar dattijai, Sanata Uba Sani.

Dumbin masu zanga-zangar da suka mamaye wasu titunan birnin Kaduna sun zargi Sanata Sani da rashin nuna kwazo a majalisa.

Taron zanga-zangar, Wanda aka fara da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar Juma'a, ta yi farin jini a wurin matasa.

Masu zanga zangar sun fara tattaruwa daga unguwar Rigasa, karamar hukumar Igabi, kafin su dunguma zuwa birnin Kaduna dauke da takardu masu nuna sakon gajiya da Sanata Sani a matsayin wakilinsu.

KARANTA: FG: Adadin allurar rigakafin korona da kowacce Jiha za ta samu

Daga cikin irin sakonnin da ke jiki takardun da matasan ke dauke da su akwai masu nuna cewa; "bama bukatar Uba Sani", "Uba Sani ya bamu kunya", da sauransu.

Kaduna: Masu zabe sun yi zanga-zangar neman a dawo da Sanata Uba Sani, sun fadi dalili
Kaduna: Masu zabe sun yi zanga-zangar neman a dawo da Sanata Uba Sani, sun fadi dalili @Ubasani
Asali: Twitter

KARANTA: Buhari ya bayar da dalilai hudu na kawo karshen Boko Haram a cikin shekarar nan

A cewar wasu daga cikin matasan, sun shirya zanga-zangar ne bayan sun gano cewa Sanata Sani ya toshe duk wata kafar sadarwa da za'a tuntubarsa sannan kuma bai kara komawa mazabarsu ba tun bayan zabensa a 2019.

Kazalika, sun zarge shi da zama dan kallo da dumama kujera a majalisa kafin daga bisani ma ya matsa laya, a daina ganinsa gaba daya a zauren majalisa

Jaridar Daily Nigerian ta ce Sanata Sani bai amsa sakon da ta aika masa domin jin ta bakinsa akan zargin da masu zanga-zangar ke yi masa ba.

A baya Legit.ng Hausa ta rawaito cewa fadar shugaban kasa ta yi raddi tare da yi wa jam'iyyar adawa ta PDP kaca-kaca.

A wani jawabi da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya fitar, fadar shugaba kasa ta ce duk wani sauran tasiri da PDP keda shi ya kare saboda ta zama jami'ar karya, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

A cewar fafa shugaban kasa, jam'iyyar PDP ba ta yi komai ba a tsawon mulkinta na shekaru goma sha shidda bayan assasa cin hanci da rashawa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel