Elon Musk ya na kan gaba a sahun fitattun Masu kudin shekarar 2021

Elon Musk ya na kan gaba a sahun fitattun Masu kudin shekarar 2021

Yayin da aka shigo sabuwar shekara ta 2021, har an fara tseren dukiya tsakanin manyan attajiran Duniya.

Elon Musk shi ne na farko a wannan jeri, inda ya doke Jeff Bezos wanda ya dade yana rike da wannan kambu.

Mun tattaro maku cikakken jerin wannan jeri, dauke da irin arzikin da su ka tara:

1. Elon Musk

Elon Musk mai shekara 49 shi ne mutumin da ya fi kowa kudi a ranar 7 ga Junairun 2021. Musk ya ba akalla Dala biliyan 188.5 baya.

Ko da ya na rayuwarsa da neman kudi kasar Amurka, Mahaifan Musk ba mutanen Amurka bane.

2. Jeff Bezos

Shugaban kamfanin Amazon, Jeff Bezos shi ne na biyu a sahun attajiran da dukiyarsu ta fito, ya mallaki abin da ya kai Dala biliyan 184.

Bezos ya saki mai dakinsa a 2019, wanda a sanadiyyar rabuwarsu, ta tafi da dinbin dukiyarsa.

KU KARANTA: Musk ne ya fi kowa kudi a 2021

3. Bill Gates

Bill Gates ya fi kowa dadewa a sahun attajiran Duniya. Abin da shugaban kamfanin na Microsoft ya mallaka ya haura Dala biliyan 132.

Masu bin sahun attajirin sun ce Gates ya yi kyauta da fiye da Dala biliyan 30 daga cikin kudinsa.

4. Bernard Arnault

Bernard Jean Étienne Arnault ya yi kudi da kamfaninsa na Louis Vuitton SE. Maganar da ake yi, yanzu Attajirin ya na da Dala biliyan 114.

Arnault wanda dukiyarsa ta karu sosai a 2018 shi ne wanda ya fi tsufa a jerin wadannan attajirai.

KU KARANTA: Bill Gates ya rasa gane kan barnar COVID-19 a Afrika

Elon Musk ya na kan gaba a sahun fitattun Masu kudin shekarar 2021
Elon Musk Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

5. Mark Zuckerberg

Mark Zuckerberg wanda ya yi fice da Facebook shi ne Attajiri na biyar a Duniya. Za a samu dala biliyan 99.9 a asusun bankin Zuckerberg.

A farkon shekarar 2019, Facebook ya hade da takwarorin manhajojin Instagram da Whatsapp.

A ranar Alhamis mun tattaro maku wasu abubuwa 4 da ya kamata ka sani game da Elon Musk wanda ya fi kowa kudi a ban kasa.

Bincike ya tabbatar da cewa Musk shi ne mutumin da ya sha gaban kowa Attajiri arziki a 2021

Musk ya yi karatu a jami’ar Queen’s University ta Ontario, jami’ar University of Pennsylvania a Philadelphia da jami’ar Stanford a Amurka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel