Mai nema yana tare da samu: Labarin tallar magungunan Sir Abba Farmer

Mai nema yana tare da samu: Labarin tallar magungunan Sir Abba Farmer

- Abba Farmer ya fara sana’ar saida magani da rancen jarin N10, 000

- Tafiya tayi tafiya, har wannan matashi ya bude shagon saida magani

- Matashin da ya soma neman kudi da N10, 000 ya ba dubunnai baya

Wani Bawan Allah mai suna Abba Farmer a shafin Twitter, ya bada labarin yadda wani abokinsa ya taimaka masa ya shiga kasuwanci, har ya yi nisa.

Sir Abba Farmer ya ce ya fara sana’ar saida magani ne da aron N10, 000, a yanzu kuwa ya na da magani guda tal wanda farashinsa ya haura N10, 000.

@SirAbbaFarmer ya ce: “Akwai wani na kusa da ni sosai, irin mutanen da ba za su bada kai ba. Na nemi ya ba ni aron kudi, ina so in fara kasuwanci.”

Ya tambayi ne wani irin kasuwanci nake so, sai na ce masa ‘kowane’. Ya bani aron N10, 000 sai na tafi. Bayan kwana biyu, na fada masa ban samu sana’ar da zan yi ba.”

KU KARANTA: An kashe wani mutumi a kamfanin aikin shinkafa a Kano

A haka wannan aminin na sa ya sake taimakawa @SirAbbaFarmer da shawarwarin kasuwanci.

Bayan kwana biyu na tambaye sa ‘Me zai hana ka bar ni in juya kudina a shagon ka (yana da shagon saida magunguna), ya yarda zan rika saida wasu magunguna.”

Abber Farmer da abokinsa suka amince zai rika sayo masa kasuwa.

SirAbbaFarmer ya ce abokinsa ya kyale shi ya zabi irin magungunan da zai saida kamar su Paracetamol, ACT, ampiclox, Vitamin c, da Procold.

KU KARANTA: Abubuwa sun jagawalgwale, Hukuma za ta je Kotu da 'Dan wasan Real Madrid

Mai nema yana tare da samu: Labarin tallar magungunan Sir Abba Farmer
Sir Abba Farmer Hoto; Twitter Daga: @SirAbbaFarmer
Source: Twitter

Wata rana sai ya aike ni kasuwa sau biyu a rana. Baya wata daya, wannan N10, 000 ta zama N25, 000, bayan shekaru daya, sai ga ni ina da N250, 000.

Yanzu maganar da aka yi wannan matashi ya bude shagonsa na kansa, ya na kuma shirin bude wani sabon shago na biyu da yake saida magunguna.

Dazu kun ji cewa wasu dakarun sojojin tsaro na jungiyar Amotekun sun kai wa Fulani hari, wanda ya yi sanadiyyar kashe wani mutum da 'yara biyu.

Sojojin Amotekun sun afkawa mutumin ne ana tsakiyar shirin bikin auren 'ya 'yan na sa biyu.

Rahotanni sun nua 'Yan sandan jihar Oyo sun tabbatar da faruwar hakan kuma sun nemi jagoran tawagar na Amotekun amma ba su iya samun shi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel