Bidiyo: Alkali zai binciki Benzema bisa zargin jefa Valbuena a tsaka mai wuya

Bidiyo: Alkali zai binciki Benzema bisa zargin jefa Valbuena a tsaka mai wuya

- Karim Benzema zai shiga kotu a kan lamarin Mathieu Valbuena a kasar Faransa

- Ana zargin Benzema da yunkurin fallasa wani bidiyo da Mathieu Valbuena ya fito

- Benzema ya nemi kudi a hannun Valbuena domin a boye bidiyon badalar da ya yi

‘Dan wasan Real Madrid, Karim Benzema zai bayyana a kotu bisa zargin yi wa Mathieu Valbuena barazana a kan wani bidiyon badala da ya fito.

AFP ta ce a ranar Alhamis, 7 ga watan Junairu, 2020, hukumomin kasar Faransa suka bayyana cewa za ayi binicike a kan ‘dan wasan kwallon.

Karim Benzema bai sake bugawa Faransa kwallo ba tun lokacin da aka bijiro da wannan bidiyon badala da ya nuna ‘dan wasa Valbuena a 2015.

Ana zargin Benzema ya tasa abokin aikinsa Valbuena a gaba, ya bukaci ‘dan wasan ya biya kudi ko kuma ya fito da bidiyonsa ya na sheke aya.

KU KARANTA: An binciko abin da ya hallaka Maradona

‘Dan kwallon na Real Madrid mai shekara 33 ya musanya wannan zargi, yace ‘yan sanda ne suka yi kutungwilar da suka jefa shi cikin matsalar.

Wani mutumi ya kira ‘Dan wasa Valbuena wanda yanzu yake taka leda a kungiyar Olympiakos, ya na yi masa barazanar fallasa bidiyon da ya fito.

Daga nan sai Mathieu Valbuena ya yi maza ya tuntubi ‘yan sanda, ya sanar da su halin da ake ciki.

Binciken jami’an tsaron ya nuna akwai hannun Karin Benzema wajen yi wa ‘dan kwallon barazanar fito da bidiyon abin kunyar da ya yi.

KU KARANTA: Dan wasan Nasarawa United, Muhammad Hussain, ya ɓace

Bidiyo: Alkali zai binciki Benzema bisa zargin jefa Valbuena a tsaka mai wuya
'Dan wasa Karim Benzema Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A lokacin da abin ya faru, Benzema da Valbuena suna cikin tawagar ‘yan wasan kwallon kasar Faransa a gasar cin kofin Duniya na 2014 a Brazil.

A bara an samu wasu shahararrun ‘yan wasa da su ka yi ritaya daga kwallo. Mun tattaro maku 'yan kwallon da aka yi bankwana da su a 2020.

Iker Casillas yana cikin wadanda su ka yi ban-kwana da tamola a shekarar da ta wuce.

Ragowar sun hada da Vincent Kompany, David Villa, Stephan Lichtsteiner, Javier Mascherano, Lucio, Daniele de Rossi, Milan Baros, da Mario Gomez.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel