'Yan bindiga sun kai hari wani kamfanin shinkafa a Kano, sun kashe mutum 1

'Yan bindiga sun kai hari wani kamfanin shinkafa a Kano, sun kashe mutum 1

- 'Yan bindiga a ranar Asabar sun kai hari wani kamfanin shinkafa da ke jihar Kano

- Sun yi kokarin garkuwa da wani Alhaji Isa amma jajircewarsa ta sa suka harbe shi a kirji

- Bayan faduwarsa cikin jini suka yi awon gaba da motarsa inda suka yi batan dabo

Wasu 'yan bindiga a ranar Asabar da yammaci sun kai hari wani kamfanin shinkafa da ke jihar Kano inda suka kashe wani mutum mai suna Alhaji Isa Abubakar.

Jaridar HumAngle ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun tsinkayi kamfanin a ranar Asabar wurin karfe 10 na dare.

Kamar yadda ganau ba jiyau ba suka sanar, maharan sun yi kokarin garkuwa da mutumin amma jajircewarsa ce ta sa suka harbe shi.

'Yan bindiga sun kai hari wani kamfanin shinkafa a Kano, sun kashe mutum 1
'Yan bindiga sun kai hari wani kamfanin shinkafa a Kano, sun kashe mutum 1. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan auren bazawara mai shekaru 50 da bazawari mai shekaru 60 sun kayatar

"Sun yi kokarin tafiya da mutumin amma sai ya ki. Daga bisani sun fitar da shi daga motarsa sannan suka harbe shi a kirji," yace.

Ya kara da cewa 'yan bindigan sun tsere da motarsa kuma sun bar shi cikin jini sannan aka gaggauta mika shi asibiti.

Abdullahi Kiyawa, kakakin rundaunar 'yan sandan jihar Kano, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce mutumin ya rasu a asibiti sakamakon jinin da ya zubar.

A cikin kwanakin nan jihar Kano tana fuskantar hauhuwar fizgen wayoyi tare da garkuwa da mutane balle a kauyukan jihar.

KU KARANTA: Matashi ya bayyana yadda budurwarsa ta rabu da shi saboda ya ki fara 'Yahoo'

A wani labari na daban, an halaka mutane uku yayin da wani daya ya samu rauni a lokacin da wasu mayakan ta'addanci da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai hari kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno a daren Laraba, majiyoyi suka sanar.

An gano cewa 'yan ta'addan sun tsinkayi kauyen Ngunari kusa da Yankin Moromti wurin karfe 10:30 na dare a karamar hukumar Konduga inda suka kashe mutum uku.

Abubakar Kulima jami'in tsaro ne daga cikin jami'an hadin guiwa na CJTF. Ya ce maharan sun dinga harbe-harbe kuma sun yi awon gaba da dabbobi a kauyen, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel