Yanzu-yanzu: Gwamna Obaseki na PDP ya sake lallasa APC a kotu
- Bayan kayar da su a akwatin zabe, Obaseki ya sake samun galaba kan APC
- Wannan karon, kotu ta yi watsi da tuhumar da APC ta shigar kan gwamnan PDP
- Har yanzu ba'aji komai daga bangaren APC ba, ko za ta daukaka kara
Wata babbar kotun tarayya dake zaune a Abuja ta yi watsi da karar amfani da kwalin jabu da jami'yyar All Progressives Congress APC ta shigar kan gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.
Alkali Ahmed Mohammed ya yi watsi da karar nan ranar Asabar, Channels TV ta ruwaito.
APC da wani jigon APC Edobor, sun shigar da karan cewa gwamna Obaseki ya yi amfani da takardan bogi yayinda yake neman takaran gwamnan jihar da akayi ranar 19 ga Satumba, 2020.
A hukuncin da ya yanke, Alkali Mohammed yace APC sun dogara da kwafin da Obaseki ya gabatarwa INEC ba tare tuntubar jami'ar don sanin sihhancin kwalin ba.
Ya kara da cewa babu gaskiya cikin karar da APC ta shigar.
Alkalin ya kara da cewa mataimakin rajisran jami'ar Ibadan ya gabatar da hujjan cewa lallai Obaseki yayi karatu a jami'ar kuma sun bashi kwali.
KU KARANTA: FG ta dakatar da diban yan Nigeria 5,000 a hukumar NDLEA
KU DUBA: Katin zama dan kasa: Duk laifin yan Najeriya, mu canza halin mu, Minista Pantami
Gwamna Obaseki ya samu nasara a zaben gwamnan jihar Edo da ya gudana ranar 19 ga Satumba, 2020.
Obaseki ya lallasa Ize-Iyamu da kuri'u sama da 80,000 kamar yadda hukumar INEC ta sanar:
Masu zabe da aka tantance: 557,443
PDP: 307,955
APC: 223,619
Bayan zaben, jam'iyyar APC ta bayyana cewa ba zata kalubalanci sakamakon zaben a kotu ba amma za ta cigaba da tuhumar gwamnan da amfani da takardun bogi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng