Hanan Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya

Hanan Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya

- A yau 8 ga watan Janairu ne Turad Sha'aban, mijin Hanan ɗiyar shugaba Buhari ke bikin zagayowar ranar haihuwarsa

- Hanan ta wallafa hoto da zantukan soyayya da fatan alheri don taya mijin nata murnar wannan ranar

- A wallafar tata, Hanan ta ce ta yi sa’a tunda ta same shi a matsayin mijinta

Diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan, ta cika da farin ciki a yau Juma’a, 8 ga watan Janairu, kasancewarsa ranar zagayowar haihuwar masoyinta, Muhammad Turad Sha'aban.

Hanan wacce a kwanaki ne aka daura aurenta da muradin ran nata, ta wallafa rubutu a shafinta na Instagram inda ta yi wa mijin nata fatan alheri.

KU KARANTA KUMA: PDP ta shiga matsala yayinda mambobinta 2,000 suka sauya sheka zuwa APC

Hanan Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya
Hanan Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya Hoto: hanan_buhari
Asali: Instagram

Baya ga zantukar soyayya, Hanan ta kuma wallafa wani hotonta da mijinta inda ta sumbace shi a goshinsa.

Ga abunda ta wallafa a rubutun nata:

“Barka da zagayowar ranar haihuwarka ya masoyina. Kaine abokin rayuwana, mai kwantar mun da hankali kuma aminina. Alhamdulillah nayi sa’a da samunka a matsayin mijina na har abada. Ina kaunarka masoyina."

A wani labari, wasu ma’auratan Najeriya sun je Twitter ta shafin angon domin wallafa kyawawan hotunan bikin aurensu.

KU KARANTA KUMA: Rundunar tsaro ta ceto mutum 103 da aka yi garkuwa da su a Katsina, In ji Masari

A wani wallafa da yayi a ranar Alhamis, 7 ga watan Janairu, mijin ya je shafinsa na Twitter domin neman albarkar mutane, inda ya bayyana cewa kwanan nan suka raya sunnah.

Hotunan ya nuna yadda suka yi ado da kwaliyya cikin tufafi daban-daban wanda ke nuni ga zamani da kuma al’ada.

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya bar jama'a a kafar sada zumuntar zamani cike da mamaki bayan ya bada labarin rabuwarsa da tsohuwar budurwarsa.

Ya ce ta bashi na'ura mai kwakwalwa kyauta a ranar zagayowar haihuwarsa domin ya fara damfara a yanar gizo.

Kamar yadda ya bayyana a labarin, ta ce bata jin dadin albashinsa domin baya isarsu. Don haka ta bashi kyautar ne don ya shiga gungun wasu masu damfarar yanar gizo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng