Matashi ya bayyana yadda budurwarsa ta rabu da shi saboda ya ki fara 'Yahoo'

Matashi ya bayyana yadda budurwarsa ta rabu da shi saboda ya ki fara 'Yahoo'

- Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani mai suna @Ikhuoria__ ya bada labarin yadda suka rabu da tsohuwar budurwarsa

- Kamar yadda ya walllafa, ta so ya zama dan damfarar yanar gizo don har na'ura mai kwakwalwa ta siya mishi kyauta

- Ta sanar da shi cewa bata farin ciki da albashinsa don haka dole ya samo hanyar samo musu manyan kudade

Wani matashi dan Najeriya ya bar jama'a a kafar sada zumuntar zamani cike da mamaki bayan ya bada labarin rabuwarsa da tsohuwar budurwarsa.

Ya ce ta bashi na'ura mai kwakwalwa kyauta a ranar zagayowar haihuwarsa domin ya fara damfara a yanar gizo.

Kamar yadda ya bayyana a labarin, ta ce bata jin dadin albashinsa domin baya isarsu. Don haka ta bashi kyautar ne don ya shiga gungun wasu masu damfarar yanar gizo.

KU KARANTA: Hukuncin kuskure: Za a biya wani mutum N3.7bn bayan kwashe shekaru 28 a gidan kurkuku

Matashi ya bayyana yadda budurwarsa ta rabu da shi saboda ya ki fara 'Yahoo'
Matashi ya bayyana yadda budurwarsa ta rabu da shi saboda ya ki fara 'Yahoo'. Hoto daga @Ikhuoria
Asali: Twitter

A kalamansa: "Na tuna lokacin da muke soyayya da tsohuwar budurwata. Ta bani kyautar na'ura mai kwakwalwa. Na yi mamakin kyautar.

"Hakan yasa na tambayeta na menene. A take ta sanar da ni cewa albashina ne baya isarta kuma tana so in fara damfarar yanar gizo. Na ce mata ba zan iya ba.

"A wurin ta sanar da ni cewa ko in fara, ko mu rabu. Abun mamaki kuwa haka ta kwashe kayanta har da kyautar da tayi min ta bar ni, rabuwarmu kenan."

KU KARANTA: Kutse a majalisa: Rayuka 4 sun salwanta, an damke magoya bayan Trump masu yawa

A wani labari na daban, ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kashe naira biliyan 2.42 a kan tafiye-tafiye na cikin gida da kasashen ketare a 2021 yayin da fadar shugaban kasa za ta kashe N135.6 miliyan a kan lemuka kamar yadda jaridar The Cable ta gani a kasafin kudi.

A ranar 31 ga watan Disamban 2020 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan kasafin kudin kasar nan na 2021.

A kasafin kudin, jimillar kudin da aka warewa ofishin shugaban kasan na manyan ayyuka shine N3.82bn sai N2.76bn na ayyukan yau da kullum.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng