Rundunar tsaro ta ceto mutum 103 da aka yi garkuwa da su a Katsina, In ji Masari

Rundunar tsaro ta ceto mutum 103 da aka yi garkuwa da su a Katsina, In ji Masari

- Gwamnatin jihar Katsina ta ceto akalla mutum 103 da aka yi garkuwa da su

- Gwamnan jihar, Aminu Masari, ya bayyana cewa ba a biya kudin fansa don ceto mutanen ba

- Masari ya kara da cewa sai da jami’an DSS da na rundunar soji suka saka hannu wajen ceto mutanen

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a ranar Juma’a, 8 ga watan Janairu, ya bayyana cewa rundunar tsaro sun ceto mutane 103 da aka yi garkuwa da su.

Masari ya bayyana hakan ne a yayinda yake jawabi ga wasu daga cikin wadanda aka ceto a gidan gwamnati, Katsina.

KU KARANTA KUMA: PDP ta shiga matsala yayinda mambobinta 2,000 suka sauya sheka zuwa APC

Rundunar tsaro ta ceto mutum 103 da aka yi garkuwa da su a Katsina, In ji Masari
Rundunar tsaro ta ceto mutum 103 da aka yi garkuwa da su a Katsina, In ji Masari Hoto: @Governormasari
Asali: Twitter

“Hakan ci gaban shirin da aka fara da ceto daliban makarantar sakandare na kankara 344 ne.

“Mun ga damar kuma muna amfani da wasu masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ganin cewa mun yi amfani da damar da kuma dawo da tarin mutanen da aka yi garkuwa da su.

“Zuwa yanzu mun yi nasarar dawo da mutane 103 da aka yi garkuwa da su kuma har yanzu ana kokarin ceto wasu. Muna yin haka cikin sirri, don tabbatar da ganin cewa babu wanda ya raunana sannan a dakatar da ci gaban garkuwan da mutane.

“Don haka, muna aikata hakan ne tare da rundunar soji, na yan sanda da na DSS.

“Ina iya baku tabbacin cewa ba a biya yan bindigan kudin fansa ba,” in ji shi.

Masari ya bukaci mutanen da su dauki lamarin a matsayin kaddara daga Allah madaukakin sarki.

“Kun ga yadda aka ceto ku. Ba a biya kudin fansa ba. Wannan ya isa ya nuna cewa addu’a na da tasiri, ku yi hakuri, Allah ya saka maku da alkhairi kan wannan wahalhalun da kuka sha,” in ji shi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa wadanda aka ceto sun kasance mata masu shayarwa da yara daga shekaru shida zuwa 16.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta ce za a hukunta yan Nigeria da suka siyar da lambobinsu na NIN

Rahoton ya kuma nuna cewa tsoho dan shekaru 70 da soja da wani dan sanda mai yaki da ta’addanci na cikin wadanda aka ceto.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel