- Jam’iyyar APC a jihar Abia ta kara karfi yayinda ta tarbi sabbin masu sauya sheka daga PDP
- Akalla mutane 2,000 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar adawar zuwa jam’iyya mai mulki a karamar hukumar Abia ta arewa
- Tsohon gwamnan jihar, Orji Kalu ne ya tarbi sabbin mambobin jam’iyyar a ranar Alhamis, 7 ga watan Janairu
Guguwar sauyin sheka ta sake kai wa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ziyara yayinda mambobinta su 2,000 a karamar hukumar Abia ta arewa suka koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Alhamis, 7 ga watan Janairu.
A bisa wani rahoto daga jaridar The Punch, sabbin masu sauya shekar sun samu tarba a Igbere daga bulaliyar majalisar dattawa, Orji Kalu a madadin shugaban jam’iyyar, Cif Donatus Nwankpa da shugaban rikon kwarya na APC, Gwamna Mai Mala Buni.
KU KARANTA KUMA: Kyawawan masoya yan Nigeria sun raya sunnah, mutane da dama sun sanya masu albarka

PDP ta shiga matsala yayinda mambobinta 2,000 suka sauya sheka zuwa APC Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter
Kalu yayinda yake tarban sabbin mambobin jam’iyyar, ya bukaci masu sauya shekar da su yi aiki don nasarar jam’iyyar mai mulki a zaben 2023.
Cif Mascot Kalu, dan takarar APC a zaben yan majalisar wakilai a 2019 ya yaba wa masu sauya shekar a kan hukuncin da suka yanke.
KU KARANTA KUMA: EFCC ta ce za a hukunta yan Nigeria da suka siyar da lambobinsu na NIN
A halin da ake ciki, Bunch Adiele da Eze Agege, a madadin masu sauya shekar sun ce: “Mu yayanku ne da ke zama tare da yin kasuwanci a karamar hukumar Aba ta arewa.”
A wani labarin, kotun daukaka kara na Fatakwal, jihar Ribas, ta yanke hukunci cewa Sanata Seriake Dickson yana da tambayar da zai amsa a gaban Alkali.
Babban kotun kasar ta fara yanke hukunci a shari’ar da ake yi da tsohon gwamnan na Bayelsa, inda ake neman soke takarar majalisar da ya yi.
A zaman da Alkalan kotun daukaka kara su kayi a karkashin Mai shari’a U. Onyemenam, an soki hukuncin da Alkalin babban kotun tarayya ya yi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng