Kyawawan masoya yan Nigeria sun raya sunnah, mutane da dama sun sanya masu albarka

Kyawawan masoya yan Nigeria sun raya sunnah, mutane da dama sun sanya masu albarka

- Hotunan wasu sabbin ma’aurata ya janyo cece-kuce a shafin Twitter

- Yayinda mutane da dama suka yi masu addu’a, wasu sun nuna mamaki kan dalilin da zai sa su neman albarkansu

- Miji da matan sun sanya kayayyaki daban daban domin samun hotuna masu ban sha’awa

Wasu ma’auratan Najeriya sun je Twitter ta shafin angon domin wallafa kyawawan hotunan bikin aurensu.

A wani wallafa da yayi a ranar Alhamis, 7 ga watan Janairu, mijin ya je shafinsa na Twitter domin neman albarkar mutane, inda ya bayyana cewa kwanan nan suka raya sunnah.

Hotunan ya nuna yadda suka yi ado da kwaliyya cikin tufafi daban-daban wanda ke nuni ga zamani da kuma al’ada.

Kyawawan masoya yan Nigeria sun raya sunnah, mutane da dama sun sanya masu albarka
Kyawawan masoya yan Nigeria sun raya sunnah, mutane da dama sun sanya masu albarka Hoto: @HafizWalii
Asali: Twitter

A hoton farko, mutumin ya sanya kwat da wando inda ita kuma matar ta sanya doguwar riga ta zamani launin namijin. A sauran hotunan sun yi shiga ta gargajiya ne.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta ce za a hukunta yan Nigeria da suka siyar da lambobinsu na NIN

Kalli wallafar da mutumin yayi a kasa:

A daidai lokacin wannan rahoton, hotunan ya samu kimanin mutum 6,000 da suka ziyarce shi tare da sharhi daban-daban daga mutane.

Ga wasu daga cikin martanin mutane a kasa:

@SquareUmar ya ce:

“Ta yaya mutum da ya yarda da Allah zai ci gaba da kasancewa cikin imani alhalin hotunan matarsa na yawo a duniya sannan mutanen kirki da bata gari suna nuna sha’awarsu a kai? Allah ya kare mu.”

KU KARANTA KUMA: Bai kamata ya kara ko kwana daya akan mulki ba; Trump ya na kan siradin tsigewa

@iam_boas yace:

“Allah ya albarkaci auren ya dan uwana. Fatan alkhairi.”

@KabiruGbadebo ya ce:

“Allah ya sanya jin dadi, zaman lafiya, kauna da albarka a wannan gida. Yallabai, miji ka so matarka. Yallabiya, mata ki kaskantar da kanki ga mijinki. Wannan shine tsarin a takaice.”

@HafizWalii ya ce:

“Amarya da ango kun yi kyau, ina addu’an Allah ya albarkacci gidanku da so, zaman lafiya Bijahi Rasululah.”

@ba55ey ya ce:

“Ina yi maka fatan farin ciki a rayuwar aurenka yallabai!”

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya bar jama'a a kafar sada zumuntar zamani cike da mamaki bayan ya bada labarin rabuwarsa da tsohuwar budurwarsa.

Ya ce ta bashi na'ura mai kwakwalwa kyauta a ranar zagayowar haihuwarsa domin ya fara damfara a yanar gizo.

Kamar yadda ya bayyana a labarin, ta ce bata jin dadin albashinsa domin baya isarsu. Don haka ta bashi kyautar ne don ya shiga gungun wasu masu damfarar yanar gizo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel