Bai kamata ya kara ko kwana daya akan mulki ba; Trump ya na kan siradin tsigewa
- Kasar Amurka ta kunyata a idon duniya bayan wasu 'yan tawaye sun kutsa kai cikin Capitol tare da tayar da hargitsi
- Ana zargin cewa 'yan tawayen sun samu daurin gindin shugaban kasar Amurka mai barin gado, Donald Trump
- Amurkawa da yawa sun fusata tare da yin kiran a gaggayta tsige Trump kafin ya hargitsa Amurka, ya jefata cikin rikici
Jagoran 'yan jam'iyyar Democrat a majalisar dattijan kasar Amurka, Chuck Schumer, ya yi kiran a gaggauta tsige Donald Trump saboda rikicin da magoya bayansa suka haddasa ranar Laraba, 6 ga watan Janairu.
A wani jawabi da Schumer ya fitar ranar Alhamis, ya ce 'yan tawayen da suka kutsa cikin Capitol suna da daurin gindin Trump, kamar yadda AP News ta rawaito.
"Wannan cin mutunci ne da zubar da kimar kasar Amurka, wanda kuma shugabanta ya jawo mata.
"Bai kamata shugaban kasa ya cigaba da zama ofis ba, bai kamata ya kara ko kwana daya a kan kujerarsa ba," a cewar Schumer.
KARANTA: Da gyara a jawabinka na sabuwar shekara; Dattijan arewa sun aika sako ga Buhari
Kazalika, Amurkawa da yawa sun bayyana bacin ransu akan abinda ya faru a Capitol, lamarin da yasa da yawan 'yan kasar ke yin kiran a gaggauta tsige Trump kafin ya kara haddasa wata kitimurmurar.
A kalla sinadarai masu fashewa guda biyu aka gano a Washington DC sakamakon rikicin da ya barke, kamar Premium Times ta samu rahotanni daga kasar Amurka.
Kazalika, jaridar Punch ta rawaito cewa majiyarta a kasar Amurka ta tabbatar mata da mutuwar wata mata da sanarwa ta bayyana cewa ta samu rauni sakamakon harbin bindiga.
KARANTA: Kano: Rundunar 'yan sanda ta kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)
Rikici ya barke a Capitol, Washington, bayan magoya bayan shugaba Trump sun yi kutse domin dakatar da tabbatar da nasarar Joe Biden.
Jaridar The New York Times ta rawaito cewa an gano bam na farko a hedikwatar kwamitin jam'iyyar Republican da ke Beltway.
Kazalika, rahoton jaridar ya bayyana an samu wani kunshi mai cike da alamun tambaya a hedikwatar kwamitin jam'iyyar Democrat.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng