Iker Casillas, Kompany, da Villa su na cikin gwarazan da su ka yi ritaya a bana

Iker Casillas, Kompany, da Villa su na cikin gwarazan da su ka yi ritaya a bana

- A shekarar nan an samu wasu shahararrun ‘yan wasa da su ka yi ritaya

- Gwarzo Iker Casillas yana cikin wadanda su ka yi ban-kwana da tamola

- Vincent Kompany da irinsu David Villa sun bi sahu, sun daina buga wasa

A wannan shekara an samu wasu fitattun ‘yan wasan kwallon kafa da su ka yi ritaya bayan sun shafe shekara da shekaru tauraruwarsu tana haskawa.

Daga cikin wadannan ‘yan wasan kwallon kafa akwai tsohon mai tsaron ragar kungiyar Real Madrid, Iker Casillas, wanda ya koma Portugal a 2015.

Shi ma tsohon ‘dan wasan bayan Manchester City, Vincent Kompany, ya ajiye kwallo a bana. ‘Dan wasan na kasar Belgium ya bugawa City wasanni 360.

Mario Gomez ya ajiye kwallo a kungiyar Stuggart, ‘dan kwallon ya shafe shekaru 11 ya na bugawa Jamus. A bana ne kuma Essam El Hadary ya yi ritaya.

Daga cikinsu har da ‘dan wasan Jamus Andre Schurrle wanda ya daina buga tamola a shekara 30. Sai tsohon ‘dan wasan bayan Everton, Leighton Baines.

KU KARANTA: Mourinho ba ya son ana kiransa 'Special One'

Wani fitaccen tauraro a wannan jeri shi ne Daniele de Rossi. Haka masu sha’awar kallon kwallon kafa ba za su sake ganin wasan Javier Mascherano ba.

Legitt.ng ta kawo jerin ‘yan kwallon da Duniya ta yi ban-kwana da su daga wannan shekara:

1. Vincent Kompany

2. Mario Gomez

3. Essam El Hadary

4. Leighton Baines

5. Aritz Aduriz

Sauran tsofaffin ‘yan kwallon da su ka yi ritaya a bana su ne:

KU KARANTA: Malaman asibiti sun gano ainihin abin da ya kashe Maradona

Iker Casillas, Kompany, da Villa su na cikin gwarazan da su ka yi ritaya a bana
Iker Casillas ya yi ritaya a bana Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

6. Andre Schurrle

7. Iker Casillas

8. Stephan Lichtsteiner

9. Javier Mascherano

10. Daniele de Rossi

Sannan jerin na kunshe da tsofaffin ‘yan wasa da su ka ci zamaninsu irinsu ‘dan wasan bayan kasar Brazil, Lucio da kuma tsohon tauraron Arsenal, Hleb.

11. Aleksandr Hleb

12. David Villa

13. Lucio

14. Milan Baros

Kwanakin baya mun kawo maku jerin ‘Yan wasan kwallon da suka rasa dukiyarsu shekaru da yin ritaya, taurarin sun tsiyace kamar ba su taba arziki ba.

Ronaldinho wanda ya taba zama gwarzon Duniya shi ne ya fi ba kowa mamaki a jerin, an yi lokacin da $7 kadai aka samu a asusun bankinsa gaba da baya.

Daga ciki har da tsohon ‘dan wasan bayan Super Eagles Celestine Babayaro bayan ya buga wa kungiyoyin Chelsea da Newcastle United na kasar Ingila.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng