Babu wata haramtacciyar kwaya a jikin Diego Maradona a lokacin da ya mutu

Babu wata haramtacciyar kwaya a jikin Diego Maradona a lokacin da ya mutu

- Malaman asibiti sun yi bincike game da abin da ya kashe Diego Maradona

- Masanan sun tabbatar da cewa babu alamun Marigayin ya kwankwadi giya

- Matsalar koda da hanta da ciwon zuciya ne su ka taru su ka hallaka Dattijon

An gano cewa tsohon tauraron Duniya, Diego Maradona ya rasu ne a sakamakon cututtukan hanta, koda da matsalar jijiyoyi da ya yi ta fama da su.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa binciken da aka yi ya nuna babu alamu ko burbushin giya ko wasu miyagun kwayoyi a jikin marigayin.

A ranar Laraba, 23 ga watan Disamba mai binciken ya bayyana abin da ya kashe tsohon ‘dan wasan.

Mai binciken abin da ya hallaka ‘dan wasan a garin San Isidro, a birnin Buenos Aires ya wallafa sakamakon gwajin da aka yi a kan gawar marigayin.

KU KARANTA: Yadda Maradona ya yi suna a Duniya

An bukaci a gudanar da bincike a kan gawar Maradona ne domin tabbatar da cewa babu sakacin malaman asibitin da ke kula da shi a mutuwar ta sa.

Kafin tsohon kocin kwallon kasar Argetina, Maradona ya mutu, ya na fama da matsaloli da su ka hada da ciwon zuciya, ‘cirrhosis’ da matsalar koda.

Gwajin da masana su kayi ya nuna babu kwayoyi ko giya a jini ko bawalin Maradona, amma an tabbatar ya na shan magungunan kwantar da hankali.

An samu alamun magungunan cutar Ulcer da ciwon kai, da wahalar bayan-gida. Haka zalika an tabbatar cewa marigayin bai shan maganin ciwon zuciya.

KU KARANTA: Tsohon 'Dan wasan kwallo Maradona ya cika

Babu wata haramtacciyar kwaya a jikin Diego Maradona a lokacin da ya mutu
Marigayi Diego Maradona Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Diego Maradona wanda ya lashe gasar cin kofin Duniya a 1986 da kasarsa ta Argentina ya rasu ne kwatsam a ranar 25 ga watan Nuwamba ya na shekara 60.

Yanzu haka ana binciken wasu likitoci Agustina Cosachov da Leopoldo Luque da hannu a mutuwar, domin su ne ke duba marigayin lokacin a asibiti.

A binciken farko da aka yi bayan mutuwar Maradona, masana sun ce huhun sa ya cika da ruwa, sannan zuciyarsa ta samu matsala, har abin ya kai ga ajali.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng