Minista ya umarci NERC ta fadawa DisCos a dakatar da karin kudin wuta

Minista ya umarci NERC ta fadawa DisCos a dakatar da karin kudin wuta

- Ministan harkar wutar lantarki ya karyata rahoton ‘karin kudin wuta’

- Saleh Mamman ya bada umarni a dawo da tsohon farashin shan wuta

- Mamman ya umarci NERC su fadawa duk DisCos ka da a canza farashi

Ministan harkar wutar lantarki, Injiniya Saleh Mamman, ya bada umarni ga hukumar NERC cewa a ajiye maganar karin kudin shan wuta a Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Ministan ya umarci NERC ta sanar da duka kamfanonin DisCos su rika saida wuta yadda aka saba.

Ministan ya fitar da jawabi ta bakin wani hadiminsa, Aaron Artimas a ranar Alhamis, 7 ga watan Junairu.

Mista Aaron Artimas ya ke cewa an bukaci a koma farashin da ake kai tun Disamban 2020 domin a samu damar sasantawa da kungiyoyin kwadago.

KU KARANTA: An kere mota mai amfani da lantarki a Najeriya

Kara karanta wannan

Yadda Aka Yi Rabon Biredi A Wajen Wani Kasaitaccen Biki Na Gani Na Fada, Bidiyon Ya Ja Hankali

“Na bada umarni ga NERC ta sanar da duka kamfanonin raba wutar lantarki na DisCos cewa su koma kan tsarin farashin da ake kai a Disamban 2020.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ministan ya ce a dakatar da wannan sabon farashi da aka kawo, a cigaba da saida wutar lantarkin a farashin da ake kai har zuwa karshen Junairu.

Jawabin na Artimas ya ce: “Wannan zai bada dama a dabbaka matsayoyin da aka cin ma a karshen zaman gwamnatin tarayya da kwamitocin kwadago.”

Ministan ya kuma karyata rahotannin da ke yawo cewa an kara farashin wutar lantarki da 50%. “Ina so in ce wadannan rahotanni sam ba gaskiya ba ne.”

KU KARANTA: Za a daina dauke wutar lantarki a Gombe

Minista ya umarci NERC ta fadawa DisCos a dakatar da karin kudin wuta
Ministan harkar wuta Hoto: www.infoguideafrica.com
Asali: UGC

“Karya ne, abin takaici ne ace ana yada wadannan rahotanni, wanda suka rudar da jama’a.” Mamman ya ce asali ma ana yi wa wasu rukuni rahusa.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Dazu kun ji cewa kungiyar kwadago tayi fatali da bayanin da hukumar NERC ta yi a game da canjin farashi, kungiyar ba ta yarda a kara kudin wuta ba.

Ma’aikatan sun ce abin da zai faru a sakamakon tashin farashin shan lantarki ba zai yi kyau ba.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa Kwamred Ayuba Wabba ya yi barazanar za su fito su nuna rashin amincewarsu a kan karin kudin shan wuta da aka yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel