Gwamnati za ta gani a kwaryarta idan ta tabbatar da karin kudin wuta inji NLC

Gwamnati za ta gani a kwaryarta idan ta tabbatar da karin kudin wuta inji NLC

- Kungiyar NLC za ta yi ta, ta kare da Gwamnatin Muhammadu Buhari

- ‘Yan kwadago ba su goyon baya karin kudin wutar lantarki da aka yi

- NLC tace ma’aikata za su iya rasa aikinsu sanadiyyar kara kudin wuta

Kungiyar kwadago ta kasa watau NLC, ta yi barazanar za ta fito ta nuna rashin amincewarta da karin kudin shan wutar lantarki da aka yi a Najeriya.

Channels TV ta rahoto cewa NLC ta fitar da jawabi na musamman ranar Talata, 5 ga watan Junairu, ta bakin shugabanta Kwamred Ayuba Wabba.

A jawabin na sa, Ayuba Wabba ya bukaci gwamnati ta janye wannan karin da tayi, ko kuma ta fuskanci matakin da ma’aikatan Najeriya za su dauka.

Wabba ya yi tir da wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka, ya ce karin kudin wutan zai yi mummunan tasiri kan kamfanonin da ke aiki a kasar.

KU KARANTA: Jihohi sun shiga duhu bayan lalacewar tashar wuta

Shugaban ‘yan kwadagon yace karin da aka yi zai yi sanadiyyar da wasu kamfanoni za su kori ma’aikatansu, ko su koma shigo da kaya daga waje.

“Mu na kira ga gwamnatin tarayya, ta yi maza-maza ta janye wannan kyautar barka da shigowa sabuwar shekara ko mu yi masu taurin kai.” Inji NLC.

A cewar Wabba, an yi wannan kari ne ba tare da bin hanyar da ta dace yayin da ake tsakiyar tattaunawa tsakanin ‘yan kwadago da gwamnati ba.

Kungiyar NLC ta zargi hukumar NERC da raina hankalin ‘yan Najeriya da bayanin da ta yi na cewa ba a kara kudi ba, amma ta sanar da canjin farashi.

KU KARANTA: An ga bam yayin da rikici ya kaure a kasar Amurka

Gwamnati za ta gani a kwaryarta idan ta tabbatar da karin kudin wuta inji NLC
Ministan wuta, Saleh Mamman Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: Facebook

Wabba ya ce jawabin da NERC ta yi, ya nuna cewa lallai hukumar ta raina mutanen Najeriya.

A jihar Kano, kun ji cewa ma’aikata zasu sa kafar wando daya da gwamna Abdullahi Umar Ganduje bayan ya yi watsi da karin albashin da aka yi a 2019.

‘Yan kwadago suna banbami kan zaftare albashin da gwamnatin Kano ta koma yi a karshen 2020.

Abdullahi Ganduje ya koma biyan N18, 000 a matsayin mafi karancin albashi a Kano. Rahotanni sun ce ‘Yan kwadago sun fusata da wannan ragi da aka yi masu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel