Gwamna Yahaya ya dau aniyar ganin bayan matsalar wutar lantarki a Gombe

Gwamna Yahaya ya dau aniyar ganin bayan matsalar wutar lantarki a Gombe

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana aniyarsa ta ganin ya samar da wutar lantarki tabbatacciya a jihar Gombe, kasancewar rashin wutar na daya daga cikin abubuwa dake dakushe harkokin cigaban jihar.

Gwamnan wanda yake jawabi bayan karbar rahoton kwamiti na musamman da ya nada domin bincike a kan ainihin matsalar lantarkin jihar, ya ce an kafa wannan kwamitin ne domin gano bakin zaren matsalar wutar lantarki a Gombe.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: Gwamnatin Ekiti za ta soma biyan N30,000 mafi karancin albashin a watan Oktoba

Inuwa wanda ya sake fadin muhimmiyar rawar da wutar lantarki ke takawa ta bangaren tattalin arziki da kuma cigaban al’umma, ya ce gwamnatinsa ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta samar da tabbatacciyar wutar lantarki a jihar.

Ya kuma kara da cewa, ganawar da yayi da shugaban kamfanin TCN ya ba shi damar fahimtar hakikanin abinda yake faruwa da wutar lantarkin arewa maso gabas.

Gwamnan yayi amfani da tattaunawar tasu inda ya bada tabbacin cewa da zarar kamfanin ya kammala wasu ayyuka a jihar Gombe da kuma sauran jihohin yankin arewa maso gabas, samun wutar zai karu a jihar tasa.

Inuwa ya ce: “Gwamnatinmu za ta cigaba da hada hannu da masu ruwa da tsaki kan lamuran wutar lantarki domin samar da wuta a jihar Gombe.”

Da yake jinjinawa kwamitin wutar lantarkin, Gwamna Inuwa ya yi alkawarin cewa nan bada jimawa ba zai kaddamar da shawarwarin da kwamitin ya rubuta masa a cikin rahoton nasu.

A bangaren guda kuwa, Engr. Bello Abdullahi Gwarzo wanda shi ne shugaban kwamitin ya yi kira ga gwamnan na ya bude hukumar kula da wutar lantarki mallakar gwamnatin jihar domin lura da wani bangare na lantarkin jihar.

https://tribuneonlineng.com/governor-yahaya-vows-to-take-gombe-out-of-darkness/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng