An kammala ƙera motocin farko masu amfani da wutar lantarki a Najeriya

An kammala ƙera motocin farko masu amfani da wutar lantarki a Najeriya

- Wani kamfani a Najeriya mai suna JET Motor Company ya kirkiro mota mai amfani da wutar lantarki da za ta yi tafiyar kilomita 300 da caji

- Kamfanin ya samu tallafin kudi na dala miliyan 9 (N3,487,500,000) daga kasar Kanada, tare da jaddada bukatar neman tallafin gwamnatin kasar nan.

- Motar ƙirar bas da ake kira JET EV, ana iya tsara ta don dacewa da bukatun amfani daban-daban

Da alama dai Najeriya ta karbi sabon salon yayi na zamani yayin da wani kamfani a kasar mai suna JET Motor Company, ya kera mota ta farko mai amfani da wutar lantarki.

A cewar wani shafi mai wallafa labarai kan al'amuran da suka shafi Najeriya a shafin sada zumunta na Twitter mai suna Naija Stories, motar ƙirar bas ana kiranta da JET EV.

Shafin Naija Stories a ranar Laraba, 22 ga watan Yuli, ya wallafa cewa motar ta yi tafiya ta tsawon kilomita 300 daga Legas zuwa Benin domin tabbatar da ingancin rikon cajinta.

Gabanin dora motar a kan hanya wajen tabbatar da ingancinta, kamfanin ya samu tallafin kudi na dala miliyan 9 (N3,487,500,000) daga wata cibiyar samar da ci gaba a Afrika ta kasar Kanada.

An kammala ƙera motocin farko masu amfani da wutar lantarki a Najeriya
An kammala ƙera motocin farko masu amfani da wutar lantarki a Najeriya
Asali: Twitter

An bude kamfanin JET Motor a shekarar 2017, inda bayan shekaru biyu ya fara kera jerin motoci da ake kira JET Mover wanda ana iya sauya fasalin cikinsu gwargwadon ra'ayin mabukata.

Darektan saye da sayarwa na kamfanin, Rupani Sanjay, ya ce ana iya tsara cikin motocin daidai da manufa kamar na bas din yawon shakatawa da tafiye-tafiye, daukar kaya, kiwon lafiya ko kuma tsarin motar makaranta da sauransu.

Mista Sanjay ya kara da cewa, motar tana iya rufa tafiya mai nisan kilomita 300 bayan an yi mata caji.

KARANTA KUMA: Masu cin moriyar shirin N-Power 14,020 ana biyansu albashi a wasu hukumomin gwamnati

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Otal din Dolce Hanoi Golden Lake da ke Vietnam ya bayyana a matsayin otal na farko a duniya da aka yi wa fenti da zinari.

Ba a dade da bude otal din ba don masu ziyara. An bayyana kayan alatun da ke cikinsa inda da yawa daga cikinsu aka kawata su da zinari.

Daga cikin akwai kwamin wanka na zinari, masai na zinari da ababen cin abinci na zinari.

Babban otal din na nan a kusa da tafkin Giang Vo a tsakiyar garin Hanoi, babban birnin Vietnam.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel