Tsarin zaben Amurka yafi na kasashen duniya ta uku muni -Trump

Tsarin zaben Amurka yafi na kasashen duniya ta uku muni -Trump

- Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kalubalanci hukumar zaben kasar da rashawa

- Shugaban ya siffanta zaben kasar mafi muni fiye da na kasashe masu tasowa

- Har wa yau shugaban ya ki amincewa da sakamakon zaben da hukumar ta fitar cewa ya sha kaye

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tsarin zaben kasar ya fi na kasashen duniya ta uku muni.

Kasashen Duniya ta Uku sune kasashe masu tasowa na Afirka, Asiya, Latin Amurka, da Australia/Oceania.

Trump ya fadi haka ne ta shafinsa na Twitter a ranar Laraba, don nuna adawarsa ga kayen da ya sha a hannun dan takarar Democrat Joe Biden a zaben shugabancin Amurka.

Jaridar PUNCH a baya ta bada rahoton cewa Joe Biden na Jam'iyyar Democrat ya lashe zaben farko a zagaye na biyu na Georgia, sa’o’i kadan kafin a shirya Majalisa don tabbatar da zababben shugaban kasa a kan Donald Trump.

KU KARANTA: Kwastam ta jaddada hana shigo da shinkafa

Tsarin zaben Amurka yafi kasashen duniya na uku muni -Trump
Tsarin zaben Amurka yafi kasashen duniya na uku muni -Trump Hoto: UGC/Vanity Fair
Asali: UGC

“Yanzunnan kawai sun samu kuri’u dubu 50 a daren jiya. Amurka na jin kunyar wautar wawaye. Tsarin zaben mu ya fi na kasashen duniya uku muni!” ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya kuma matsawa mataimakin shugaban kasar Mike Pence lamba kan ya ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar a wasu sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Trump ya ce, “Jam’iyyar Republican kuma, mafi mahimmanci, kasarmu, tana bukatar shugabanci fiye da kowane lokaci - da karfin iko. Ka kasance da ƙarfinka!

“Jihohi na son gyara kuri’un su, wanda a yanzu suka san sun dauru ne akan rashin tsari da magudi, tare da rashawa da bata taba samun amincewar majalisa ba.

"Abin da kawai Mike Pence zai yi shi ne a mayar da su zuwa Jihohin, KUMA MUN YI NASARA. Ka aikata Mike, wannan lokaci ne na tsananin ƙarfin hali! ”

Da yammacin ranar Laraba, ana sa ran Pence zai jagoranci wani taron hadin gwiwa na Majalisar don tabbatar da zaben Kwalejin Zabe wanda ya tabbatar da Biden a matsayin wanda ya lashe zaben Fadar White House.

Kafofin yada labaran Amurka sun bayar da rahoton cewa Trump na shirin yin jawabi a kusa da Fadar White House don nuna rashin amincewa a kan takardar shedar, tare da daruruwan magoya bayansa a sanye da huluna dauke da rubutun "Make America Great Again".

KU KARANTA: Haɗari ne gabatar da allurar rigakafin COVID-19 a Najeriya yanzu - Masanan Kwayar Cuta

Tuni suka taru a tsakiyar gari yayin da 'yan sanda su ma suka halarta, yayin da masu shaguna suke tsoron tashin hankali.

Zanga-zangar na zuwa ne kwanaki kadan bayan an ji shugaban mai shekaru 74 a cikin kaset yana neman jami’an Georgia da su soke sahihancin zaben da aka gudanar a watan Nuwamba tare da ba shi nasara a jihar.

A wani labarin, A ranar Litinin ne Charlie Baker, gwamnan jihar Massachusetts da ke kasar Amurka, ya bukaci wasu jami'an tsaro na musamman guda 1,000 a kan su kasance cikin shirin ko ta kwana koda za a samu hargitsi a zaben kasar ranar Talata.

A jihar Oregon kuwa, gwamna Kate Brown ta saka dokar ta baci a yankin Portland bisa tunanin samun yiwuwar barkewar rikici sakamakon zaben da ake gudanarwa ranar Talata, kamar yadda Punch ta rawaito.

A karkashin dokar ta bacin, rundunar 'yan sandan jihar Oregon da babban jami'in tsaro na yankin Multnomah zasu tabbatar da tsaro da zaman lafiyar jama'a a Portland.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.