Kotun Iraqi ta ba da sammacin damke Donald Trump

Kotun Iraqi ta ba da sammacin damke Donald Trump

- Kotun Bagadaza ta bada sammacin kame Donald Trump da zargin bada umarnin hari da jirgi mara matuki

- Kotun ta bayyana hukuncin da ta tanada ga duk wanda yayi kisa da gangan kamar yadda Donald aikata

- Kotun ta bayyana tana ci gaba da bincike don gano wasu masu hannu a kisan

Kotun Bagadaza ta ba da sammacin kame Shugaban Amurka Donald Trump a wani bangare na binciken da take yi game da kisan wani babban kwamandan sojojin Iraqi.

Abu Mahdi al-Muhandis, mataimakin shugaban kungiyar ta Iraqi da ke goyon bayan Iran Hashed al-Shaabi, ya mutu a wannan harin da Amurka ta kai.

A harin ne janar din Iran Qasem Soleimani ya mutu a filin jirgin saman Bagadaza a ranar 3 ga Janairun bara.

Trump ne ya ba da umarnin harin da jirgi mara matuki a kan ayarin motocinsu, wanda daga baya ya fitar da bayanin cewa hakan daukar fansar "maza biyu a kan farashin daya" ne.

KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya yi wa makusantansa a mulki garanbawul - Magoya bayan APC

Kotun Iraqi ta ba da sammacin kwamushe Donal Trump
Kotun Iraqi ta ba da sammacin kwamushe Donal Trump Hoto: Facebook/Daily Trust
Asali: Facebook

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman game da zartar da hukunci, taƙaitawa ko zartar da hukunci ba tare da izini ba, Agnes Callamard, ya bayyana tagwayen kashe-kashen a matsayin "bijirewa" kuma "haramun".

Iran ta riga ta bayar da sammacin kamo Trump a watan Yuni, kuma ta nemi Interpol ta ba da ita a matsayin abin da ake kira 'red notice' ga sauran rundunonin ‘yan sanda a duk duniya, bukatar da har yanzu ba a samu ba.

Kotun da ke gabashin Bagadaza ta ba da sammacin kame Trump ne a karkashin sashi na 406 na kundin hukunta laifuka, wanda ya tanadi hukuncin kisa a duk shari’ar kisan kai da gangan, in ji masu shari’ar.

Kotun ta ce an kammala binciken farko amma "ana ci gaba da bincike don gano sauran masu laifi a wannan lamarin, walau 'yan Iraki ne ko kuma baƙi."

KU KARANTA: Pantami: Shin za a rufe layin wadanda basu hada SIM dinsu da NIN ba?

A yayin da ake shirye-shiryen bikin tagwayen kashe-kashen ranar Lahadi, bangarorin da ke goyon bayan Iran sun kara zage damtse kan Washington da jami’an Iraki da ake ganin sun hada baki da su.

A wani labarin daban, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tsarin zaben kasar ya fi na kasashen duniya ta uku muni. Kasashen Duniya ta Uku sune kasashe masu tasowa na Afirka, Asiya, Latin Amurka, da Australia/Oceania.

Trump ya fadi haka ne ta shafinsa na Twitter a ranar Laraba, don nuna adawarsa ga kayen da ya sha a hannun dan takarar Democrat Joe Biden a zaben shugabancin Amurka.

Jaridar PUNCH a baya ta bada rahoton cewa Joe Biden na Jam'iyyar Democrat ya lashe zaben farko a zagaye na biyu na Georgia, sa’o’i kadan kafin a shirya Majalisa don tabbatar da zababben shugaban kasa a kan Donald Trump.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel