Ya kamata Buhari ya yi wa makusantansa a mulki garanbawul - Magoya bayan APC

Ya kamata Buhari ya yi wa makusantansa a mulki garanbawul - Magoya bayan APC

- Wani jigo a kungiyar magoya bayan jam'iyyar APC ya kalubalanci tsarin tafiyar mulkin Buhari

- Jigon ya bayyana cewa ba sa jin dadin maganganun jama'a a kan mulkin Shugaban kasan

Ya kirayi shugaba Buhari da ya aikata wani abun da zai sa 'yan jam'iyyar bugun kirji yayin tallata jam'iyyar

Magoya bayan Jam’iyyar APC karkashin inuwar hadakar kungiyoyin magoya bayan APC, a ranar Laraba, sun sake yin kira ga Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), da ya maye gurbin shugabannin ma’aikata.

Kungiyar ta ce al'amuran jihohi a halin yanzu a kasar musamman yadda ya shafi lafiyar rayuka da dukiyoyi na sanya yan kungiyar da ke da kishin yin gaskiya gagara kare mulkinsa.

KU KARANTA: Masu amfani da wutar lantarki sun ki amincewa da karin harajin wuta

Ya kamata Buhari ya yi wa makusantansa a mulki garanbawul - Magoya bayan APC
Ya kamata Buhari ya yi wa makusantansa a mulki garanbawul - Magoya bayan APC Credit: APC
Source: Facebook

Wannan ya na kunshe ne a cikin wani sako da Sakataren yada labarai na kungiyar na kasa, Sam Oburu, ya sanya a bangon Facebook dinsa.

Wasikar ta ce, “Abin yana da matukar wuya kuma yana sanya mu zama wawaye yayin tallata wannan gwamnatin ta mu ta PMB, ba tare da kai Shugaban kasa ka yi wani abun a zo a gani ba da kwazo don kara wa ‘yan Nijeriya kwarin gwiwa.

“Muna duba zuwa 2023, ya kamata mu iya bugun kirji cewa muna da Shugaban kasa mai sauraron mu.

“Shawarata ya Shugaban kasa, ya kamata ka yi daya daga cikin wadannan biyun da wuri-wuri: Canja shugabannin tsaro ko kuma canzawa tare da yi wa ministocinka garambawul, ko kuma ka yi duka biyun.

KU KARANTA: Tsarin zaben Amurka yafi na kasashen duniya ta uku muni -Trump

“Ya kamata mu yi wani abu mai kyau don tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa muna aiki mai kyau.

"Ina son Shugaban kasa na kuma ina kaunar jam'iyyata ta APC amma labaran da muke ji kan titi ba su da dadi."

A wani labarin daban, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi ikirarin cewa yan Nijeriya sun kagu don ganin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta karbe mulki daga hannun All Progressives Congress (APC) a 2023 domin yin shugabanci nagari.

Wani jawabi da Kelvin Ebiri, hadimin labaran Wike ya sa hannu sannan Legit.ng ta gano a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu ya nuna cewa gwamnan na Ribas ya bayar da tabbacin ne a wajen bikin kaddamar da wani aikin gina hanya.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume, shahararren sanatan APC shine ya kaddamar da aikin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel