NLC ta harzuka, Ganduje ya daina biyan N30, 000 a matsayin mafi karancin albashi

NLC ta harzuka, Ganduje ya daina biyan N30, 000 a matsayin mafi karancin albashi

- Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da biyan sabon tsarin albashi na N30, 000

- Abdullahi Ganduje ya koma biyan N18, 000 a matsayin mafi karancin albashi

- ‘Yan kwadago sun fusata da wannan ragi da aka yi wa ma’aikatan jihar Kano

Daily Trust ta ce ma’aikatan gwamnatin Kano sun samu kansu a wani irin hali bayan gwamnati ta zaftare masu albashin watannin Nuwamba da Disamba.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya koma biyan albashin da ne, amma wasu ma’aikata sun ce sun karbi abin da bai kai ko da N18, 000 ba.

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta rage albashin ma’aikatan na ta ne a sakamakon karancin kudin da ta ke samu daga kason FAAC saboda matsalar tattalin arziki.

Ma’aikata sun koka da wannan ragin da aka yi masu, suka ce bai kamata a rage albashinsu yayin da ake shirin batar da N2.3bn a zaben kananan hukumomi ba.

KU KARANTA: Jihar Gombe za ta cigaba da biyan N30, 000

Jaridar ta ce wasu ma’aikata sun shiga tambayar abin da Abdullahi Umar Ganduje ya ke yi da kason FAAC, kudin shiga da gudumuwar da ake samu daga waje.

Hadimin gwamnan, Salihu Tanko Yakasai, ya ce an daina biyan N30, 000, an komawa tsohon tsarin N18000 ne saboda matsin lambar tattalin arziki da aka shiga.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya yi irin wannan bayani, ya ce halin da aka shiga a Najeriya ya sa aka koma zaftare albashin.

Jaridar ta nemi tuntubar shugaban ma’aikatan gwamnatin Kano, Binta Ahmed, abin bai yiwu ba.

KU KARANTA: Zulum ya fara biyan mafi karancin albashi a Borno

NLC ta harzuka, Ganduje ya daina biyan N30, 000 a matsayin mafi karancin albashi
Gwamna Ganduje Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wadanda ragin ya shafa sune ainihin ma’aikatan gwamnati 55, 505 da sauran ma’aikatan makarantu da hukumomin jihar Kano da kuma mukarraban gwamna.

A lokacin da ake kukan babu kudi, sai ku ka ji cewa shugaba Muhammadu Buhari zai farantawa tsofaffin Ma’aikatan gwamnati rai, ya umarci a fito masu da fanshonsu.

Rahotanni sun ce gwamnatin tarayya ta warewa ‘yan fansho kudin da su ke bi har N11.82bn.

Hukumar PenCom ta ce za a biya hakkokin wasu tsofaffin ma’aikata ne da su ka yi aiki a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya shekarun da suka wuce.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel