Tashan wutan lantarki ta kasa ta lalace, sunayen jihohin da rashin wuta zai shafa

Tashan wutan lantarki ta kasa ta lalace, sunayen jihohin da rashin wuta zai shafa

- Babbar tashar wutar lantarki ta lalace, kuma hakan zai kawo cikas ga wutar lantarkin wasu jihohi

- Jihohin da rashin wutar zai shafa sun hada da jihar Kaduna, Sokoto, Kebbi da jihar Zamfara

- Shugaban yada labarai na kamfanin rarrabe wutar lantarki na jihar Kaduna ya sanar da hakan

Abdulazeez Abdullahi, shugaban yada labarai na kamfanin rarrabe wutar lantarkin jihar Kaduna, ya tabbatar da aukuwar wani lamari a wata takarda da ya gabatar ranar Lahadi, The Cable ta wallafa.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, Abdullahi ya sanar da lalacewar tashar samar da wutar lantarki ta kasa, da misalin karfe 11:26 na safiyar Lahadi.

Kamar yadda ya wallafa, "Muna masu takaicin sanar muku da za ku fuskanci rashin wutar lantarki a jihar Kaduna, Sokoto, Kebbi da jihar Zamfara, sakamakon lalacewar tashar rarrabe wutar lantarki ta kasa. Al'amarin ya faru ne da misalin karfe 11:26 na safe."

KU KARANTA: Ni ce budurwar da ke fita da saurayinta ta kashe masa N7000 ba tare da ta fadi ba, Budurwa

Tashan wutan lantarki ta kasa ta lalace, sunayen jihohin da rashin wuta zai shafa
Tashan wutan lantarki ta kasa ta lalace, sunayen jihohin da rashin wuta zai shafa. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

"Za mu yi kokarin tabbatar da gyarawa cikin gaggawa. Muna fatan za a gafarcemu."

Haka kuma kamfanin rarrabe wutar lantarki na Eko, (EKEDC) sun tabbatar da lalacewar tashar wutan, har suka tura wa mutane sako a ranar Lahadi.

"Muna masu takaicin sanar da ku lalacewar tashar wutar lantarki ta kasa, za a fuskanci rashin wuta na wani lokaci.

"Muna yin iyakar kokarin gyaran TCN din mu don samar da wutar lantarki. A gafarcemu," yace.

KU KARANTA: Fitacciyar jaruman fim ta ce karenta ya fi mata kawayenta masu tarin yawa

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya fatattaki wasu jami'an kula da kananun hukumomi 2. Dama ya fara fatattakar ma'aikata tun bayan ya canja sheka.

Ya kori Okorie Daniel na Ivo DC da Fabian Ivoke na Echiele DC, saboda kin amincewa da wata takarda da suke tunanin za ta bata sunan tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel