2023: Yan Nigeria na jiran PDP ta karbi mulki, in ji Wike yayinda ya karbi bakuncin sanata Ndume

2023: Yan Nigeria na jiran PDP ta karbi mulki, in ji Wike yayinda ya karbi bakuncin sanata Ndume

- Gwamna Wike ya aika wani muhimmin sako zuwa ga jam’iyyar APC mai mulki gabannin zabe na gaba a 2023

- Gwamnan na jihar Ribas wanda ya karbi bakuncin Sanata Ndume don kaddamar da wani aiki ya ce jam’iyyar mai mulki ta shirya mikawa PDP mulki a 2023

- Kasancewar Sanata Ndume, jigon APC a jihar Ribas da abunda ya fadi game da Gwamna Wike ya haddasa rade-radi a kan yunkurinsa na gaba

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi ikirarin cewa yan Nijeriya sun kagu don ganin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta karbe mulki daga hannun All Progressives Congress (APC) a 2023 domin yin shugabanci nagari.

Wani jawabi da Kelvin Ebiri, hadimin labaran Wike ya sa hannu sannan Legit.ng ta gano a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu ya nuna cewa gwamnan na Ribas ya bayar da tabbacin ne a wajen bikin kaddamar da wani aikin gina hanya.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume, shahararren sanatan APC shine ya kaddamar da aikin.

2023: Yan Nigeria na jiran PDP ta karbi mulki, in ji Wike yayinda ya karbi bakuncin sanata Ndume
2023: Yan Nigeria na jiran PDP ta karbi mulki, in ji Wike yayinda ya karbi bakuncin sanata Ndume Hoto: Gov Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Gwamna Wike ya ce yan Najeriya sun bunkasa kokensu na shugabanci mai kyau, tattalin arziki mai inganci da kuma ayyukan ci gaban da PDP ke ci gaba da samarwa a jihohin da take shugabanci.

KU KARANTA KUMA: Fina finan Hausa 8 da suka shahara a 2020: Jerin sunaye da masu daukar nauyi

Ya jadadda cewa PDP na aiki a jihar Ribas da sauran jihohin da babbar jam’iyyar adawar ke jagoranci.

Don haka gwamnan ya bukaci sanata Ndume da APC da su mutunta muradin yan Najeriya wadanda ke son dawowar PDP mulki a 2023 don samar masu da damokradiyyar da suke so.

Ya ce:

“Zuwa ga babban bakonmu (Ndume), kada yayi fushi saboda za mu karbi mulki daga hannunsu. A lokacin da suka zo, bamu yi fada ba, sun karbe mulki. Yanzu yan Najeriya sun yanke shawarar canja su, suma sai su gaggauta mika mana mulki ba tare da kowani fada ba.”

A nashi martanin, Sanata Ndume ya ce ya ji dadin karamcin da aka nuna na bashi damar aiwatar da wannan aiki da kuma kasancewa cikin abunda Gwamna Wike ke yi wa jiharsa.

Ya bayyana Gwamna Wike a matsayin dan kasa na gaskiya wanda muryarsa ke da muhimmanci a harkokin kasa, kuma mutum mai fadin gaskiya a kan shugabanci.

Ndume ya kuma ci gaba da jinjinawa gwamnan na jihar Ribas, inda ya bayyana shi a matsayin dan kasa wanda ke fadin gaskiya ta bangaren mulki.

Ya ce:

“Sannan daga yau, ka kwana da sanin cewa kai shugaba ne a kasar nan. Da ace kai ba aboki kuma dan kasa bane, da ba zan kasance a nan ba, Fayemi da sauran gwamnonin APC da dama ba za su kasance a nan ba.

“Ka kasance daya daga cikin yan Najeriya na gaskiya da na taba sani. Kuma idan muna da mutane irinku da ke fadin gaskiya a mulki, Najeriya za ta inganta garemu mu dukka.”

Da wannan ziyara da ruwan yabo da ya kwararo kan Gwamna Wike wanda yayi kaurin suna wajen sukar APC, za a koma yin rade-radi game da yunkurin siyasar Sanata Ndume na gaba ta a kasar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Katsina ta ce lallai bata biya kudin fansar sakin daliban Kankara ba

A wani labarin, an yi watsi da wani rahoto da ke ikirarin cewa wasu gwamnoni daga yankin kudu maso gabas na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar All progressives Congress (APC).

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa babu wani gwamna a karkashin inuwarta daga kudu maso gabas da ke tunanin sauya sheka zuwa kowace jam’iyya.

A cewar jaridar This Day, mataimakin Shugaban jam’iyyar a yankin, Ali Odefa, shine ya bayyana hakan a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Awka, a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel