Amsar Rahama Sadau game da batun dena fim bayan aure

Amsar Rahama Sadau game da batun dena fim bayan aure

- Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta nuna alamun ba dole ta dena fim ba idan ta yi aure

- Rahama Sadau ta ce bata san dalilin da yasa ake tsangwamar mata da ke sana'ar fim ba amma ake kyalle wasu matar

- Jarumar ta bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyi daga masoyanta a shafin Twitter a ranar Laraba

Fitacciyar jarumar fina-finai na Kannywood Rahama Sadau na da ja game da batun dena yin fim idan ta yi aure, inda ta nuna alamun ba dole bane ta dena fim idan ta yi aure.

Jarumar mai shekaru 27 ta bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da ta ke amsa tambayoyin masoyanta a shafin sada zumunta na Twitter.

Amsar Rahama Sadau game da batun dena fim bayan aure
Amsar Rahama Sadau game da batun dena fim bayan aure. Hoto: @Rahama_sadau
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tallafin Covid 19: 'Yan kasar Ghana za su sha wutar lantarki kyauta na watanni uku

Jarumar ta dauki mintuna 30 tana amsa tambayoyi daga masoyanta da suka shafi bangarori da yawa na rayuwarta, inda wani masoyinta ya tambayeta ko za ta dena fim idan tayi aure.

Sai ta bashi amsa da cewa, bata fahimci dalili da yasa ake tsangawar mata da ke harkar fina-finai ba idan aka kwatanta da takwarorinsu da ke wasu sana'o'in.

"Don me mutum zai dena fim saboda aure? Shin yin fim ba aiki bane? Me yasa ba a ganin laifin mata da ke wasu ayyukan sai dai yan fim? Misali kamar aikin jarida." #AskRahama

KU KARANTA: An rufe shafin Trump na Twitter, an yi barazanar dakatar da shi

Jarumar kuma ta yi magana a kan yadda al'umma ke yawan sukar ta idan ta aikata wasu abubuwan inda ta ce hakan ba adalci bane ake mata.

Duk da hakan, Rahama ta ce ra'ayoyin mutane ba zai sa ta dena harkokinta ba.

A baya-bayan nan dai wasu hotunan da jarumar ta wallafa sun janyo cece-kuce inda wasu ke ganin shigar da tayi a hotunan bai dace ba kuma ya saba wa koyarwar addinin musulunci.

An kuma taba dakatar da Rahama Sadau daga Kannywood a 2016 saboda 'rungumar' mawaki Classiq a bidiyon wakarsa.

A wani labari na daban, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bankado ayyukan almundahana a tallafin karatun kasashen waje na gwamnatin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Magaji Rimingado, wanda ya bayyana haka ga yan jarida ranar Talata, ya ce daga 2015 zuwa 4 ga Janairun 2021, gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 7 a tsarin wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata, amma ana samun korafin daliban da suka rage a kasashen waje.

Ganin yadda korafe korafe suka yi yawa kuma ya kamata ace da yawa yawancin daliban sun kammala karatun su, gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar da tayi "bibiya", bincika ta kuma dauki mataki akan badakalar", in ji Rimingado.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel