PDP ta ce babu wani gwamnan kudu maso gabas a karkashin inuwarta da ke shirin sauya sheka

PDP ta ce babu wani gwamnan kudu maso gabas a karkashin inuwarta da ke shirin sauya sheka

- Daga karshe jam’iyyar PDP ta yi martani kan wani rahoto da ke zargin shirin sauya sheka a inuwarta

- Wani jigon jam’iyyar, Ali Odefa, ya dasa ayar tambaya a kan gaskiyar rahoton

- Jigon ya ce dukkanin gwamnonin PDP a kudu maso gabas sun kasance masu biyayya ga jam’iyyar

An yi watsi da wani rahoto da ke ikirarin cewa wasu gwamnoni daga yankin kudu maso gabas na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar All progressives Congress (APC).

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa babu wani gwamna a karkashin inuwarta daga kudu maso gabas da ke tunanin sauya sheka zuwa kowace jam’iyya.

A cewar jaridar This Day, mataimakin Shugaban jam’iyyar a yankin, Ali Odefa, shine ya bayyana hakan a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Awka, a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu.

PDP ta ce babu wani gwamnan kudu maso gabas a karkashin inuwarta da ke shirin sauya sheka
PDP ta ce babu wani gwamnan kudu maso gabas a karkashin inuwarta da ke shirin sauya sheka Hoto: Prince Uche Secondus
Source: Facebook

Ya ce babu wani abun damuwa game da karfin jam’iyyar a kudu maso gabas.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Katsina ta ce lallai bata biya kudin fansar sakin daliban Kankara ba

Odefa ya bayyana cewa: “Anambra cikakkiyar jihar PDP ce...Enugu PDP ce, Abia PDP ce itama. Babu mamaki kun ji wani rade-radi cewa wani gwamna daga yankin na shirin ficewa, amma ba gaskiya bane. Babu wani gwamna da zai bar PDP.

“Duk mun san abunda ya faru a Ebonyi kuma muna farin cikin cewa gwamnan ya fice. Bama jin kowani dar; jihar ta PDP ce.”

Jigon jam’iyyar ya shawarci mambobin PDP a jihar wadanda suka shigar da kara a kan jam’iyyar da su gaggauta janye su domin amfanin jam’iyyar.

Ya ce kudirin shine don tabbatar da ganin cewa jam’iyyar ta shiga zaben gwamna na 2021 mai zuwa a Anambra kan ta a hade.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi awon gaba da matafiya 20 a Nasarawa

A wani labarin, jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ta ce rashin tausayi ne gwamnatin tarayya ta yi karin farashin wutan lantarki yayinda kasar ke cikin matsin tattalin arziki.

Jam'iyyar ta bayyana hakan a jawabin da ta saki mai taken, 'PDP ta yi watsi da guzurin sabuwar shekara na karin farashin wutan lantarki,' ranar Talata.

A jawabin, PDP ta ce wannan karin farashin zai tsananta halin da yan Najeriya ke ciki, kuma ta yi kira ga shugaba Muhammasu Buhari yayi gaggawa janye wannan kari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel