Fina finan Hausa 8 da suka shahara a 2020: Jerin sunaye da masu daukar nauyi

Fina finan Hausa 8 da suka shahara a 2020: Jerin sunaye da masu daukar nauyi

- Kamfanin Kannywood ta kasance babbar masana'antar shirya fina-finan Hausa da ke yankin arewacin kasar

- A yayinda aka shiga sabuwar shekara, Legit.ng ta waiwaya baya domin zakulo wasu manyan fina-finai takwas da suka samu karbuwa a wajen mutane

- Mun kuma kawo jerin sunayen wadanda suka dauki nauyin fina-finan

Duk da tarin kalubale da masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ke fuskanta a wannan lokaci, tana nan daram dam inda take nishadantar da masoya.

Daya daga cikin manyan matsalolin da suka addabi masana’antar shine na kasuwanci domin masu satar fasaha na hana su cin guminsu. Wannan ne ya sa suka fito da tsarin nuna fina-finansu a gidajen kallo na sinima sannan suka fito da manhajar Northflix duk don samun mafita.

Hakazalika wasu manyan masu shirya fina-finai suka fito da tsarin yin wasanni masu gajeren zango wanda suke haskawa duk mako musammana Youtube.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasar 2023: Dan kudu ne zai gaji Buhari, Osoba

Fina finan Hausa 8 da suka shahara a 2020: Jerin sunaye da masu daukar nauyi
Fina finan Hausa 8 da suka shahara a 2020: Jerin sunaye da masu daukar nauyi Hoto: The Links News
Source: UGC

Legit.ng ta kawo maku wasu manyan fina finan Hausa 8 da suka shahara a shekarar 2020 tare da wadanda suka sauki nauyinsu kamar yadda shafin @Hausafilmsnews

ta wallafa a Twitter.

Bana Bakwai, Fati, Ciwon IdanuNa:

Abubakar Bashir mai shadda ne ya dauki nauyin wadannan fina-fanai guda uku kuma sun samu karbuwa sosai a wajen ma’abota kallon fim din Hausa.

Mati A Zazzau:

Fim din Mati A Zazzau ya samu karbuwa sosai a wajen masoya kasancewar yana dauke da manyan jarumai. Rahama Sadau da Saddiq Sani Saddiq ne suka dauki nauyin sa.

Jaruma:

Fim din Jaruma wanda Mandi Brigate ta dauki nauyi shima ya samu karbuwa sosai a wajen masoyan fina-finan Hausa a 2020.

Karamin Sani:

Fim din karamin sani ma ya samu karbuwa a wajen ma’abota son fina-finan Kannywood kuma Sani Indomie ne ya dauki nauyin shiryawa.

KU KARANTA KUMA: Kashe-kashe: Masu siyasar a mutu ko ayi rai ne ke hada kai da yan bindiga don tarwatsa Nigeria, Umahi

Sarkin Barayi:

Fim din Sarkin Barayi wanda Abba Kabugawa ya shirya yana daya daga cikin manyan fina-finan Kannywood a 2020.

A wani labari na daban, Kyaftan na Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da shirin ginin katafaren makaranta a Bukuru, karamar hukumar Jos South ta jihar Plateau saboda a wajen ya girma.

Ahmed Musa ya bayyana cewa zai gina makarantan ne matsayin mayar da alherin da garin tayi masa a matsayin mahaifarsa.

A sako mai kama da martani a shafinsa na Tuwita, Ahmed Musa, ya ce bai jahilci bukatar yin hakan ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel