Kashe-kashe: Masu siyasar a mutu ko ayi rai ne ke hada kai da yan bindiga don tarwatsa Nigeria, Umahi

Kashe-kashe: Masu siyasar a mutu ko ayi rai ne ke hada kai da yan bindiga don tarwatsa Nigeria, Umahi

- Gwamnonin kudu maso gabas sun yi ikirarin cewa wasu yan siyasa ke kokarin rushe kasar

- A cewar shugaban kungiyar gwamnonin na kudu maso gabas, Dave Umahi, wadannan yan siyasa sun hada kai ne da yan bindiga don cimma mugun nufinsu

- Umahi ya kuma yi watsi da wutar fitina da wasu ke kokarin hurawa ta hanyar ikirarin cewa ana fatattakar makiyaya daga jihar Ebonyi

Kungiyar gwamnonin kudu maso gabas ta zargi masu siyasan a mutu ko ayi rai da hada kai da yan bindiga don tarwatsa Najeriya, Channels Television ta ruwaito.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, shine ya bayyana haka a ranar Talata, bayan wata ganawa da gwamnonin yankin biyar ta yanar gizo.

“Gwamnonin sun damu matuka a kan kashe-kashe da garkuwa da mutane da ke wakana a yankin kudu maso gabas, kisan mutanenmu da hukumomin tsaro,” in ji shi.

Kashe-kashe: Masu siyasar a mutu ko ayi rai ne ke hada kai da yan bindiga don tarwata Nigeria, Umahi
Kashe-kashe: Masu siyasar a mutu ko ayi rai ne ke hada kai da yan bindiga don tarwata Nigeria, Umahi Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Katsina ta ce lallai bata biya kudin fansar sakin daliban Kankara ba

“Ayyukan masu siyasan a mutu ko ayi rai shine ke kara tabarbarar da halin da ake ciki a wannan lokaci.

“Akwai masu siyasan a mutu ko ayi rai da dama a dukkan jam’iyyun siyasa wadanda suka matsu da son mulki kuma sun hada kai da wasu yan bindiga a yankin kudu maso gabas don tarwatsa kasar.”

Gwamna Umahi ya yi bayanin cewa jihohin kudu maso gabas biyar sun janye kansu daga wani taro da wasu masu ruwa da tsaki daga yankin suka shirya kan halin tsaro.

Gwamnan na Ebonyi ya bukace su da su yi magana sannan su yi watsi da kashe-kashe a yankinsu a maimakon haka.

Ya kuma yi amfani da damar wajen yin karin haske a kan wani bidiyo da ya shahara a shafin soshiyal midiya, game da korar wasu yan arewacin kasar mazauna jihar Ebonyi.

“Ahlin Fulani ne suka yanke shawarar komawa jihar Taraba da kuma barin wasun su a jihar Ebonyi kuma shakka babu, mutumin na nan har yanzu.

“Kamar yadda muka tattara daga bayanan sirri, yan siyasa sun hada murya sannan suka ce yan Igbo ne ke fatattakar makiyaya daga jihar Ebonyi.

“Wannan bidiyon ya shahara sosai sannan ya haifar da rudani a sauran yankunan kasar. Wannan bai dace ba saboda muma muna da mutanenmu fiye da miliyan 11 da ke rayuwa a arewa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan PDP ya jinjinawa shirin gwamnatin tarayya na daukar ayyuka na musamman

“Muna da mutane da yawa da ke zama a kudu maso kudu da kudu maso yamma. Idan mutane suka aika haka, suna ganin sunayi ne don bata sunan wani gwamna, basu san cewa suna yi ne domin a fara kashe mutanenmu ba.”

A wani labari, mun ji cewa an yi watsi da wani rahoto da ke ikirarin cewa wasu gwamnoni daga yankin kudu maso gabas na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar All progressives Congress (APC).

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa babu wani gwamna a karkashin inuwarta daga kudu maso gabas da ke tunanin sauya sheka zuwa kowace jam’iyya.

A cewar jaridar This Day, mataimakin Shugaban jam’iyyar a yankin, Ali Odefa, shine ya bayyana hakan a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Awka, a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel