Shugaban kasar 2023: Dan kudu ne zai gaji Buhari, Osoba

Shugaban kasar 2023: Dan kudu ne zai gaji Buhari, Osoba

- Tuni yan siyasa a kasar suka fara tattauna batun wanda zai shugabanci Najeriya bayan mulkin shugaba Buhari

- Tsohon gwamna, Olusegun Osoba, ya bayyana yarjejeniyar da shugabannin APC suka kulla game da wanda zai shugabanci kasar a 2023

- Osoba ya ambaci yankin kasar da ake sanya ran zai samar da dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba, ya bayyana cewa akwai yarjejeniyar da aka kulla a lokacin da aka kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A cewar Osoba, yarjejeniyar shine dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023 zai fito daga yankin kudu.

Da yake magana a lokacin da ya fito a shirin Arise Television, Osoba, ya ce yarjejeniyar shine cewa arewa za ta samar da Shugaban kasa a 2015, yayinda Shugaban jam’iyyar zai fito daga kudu.

Shugaban kasar 2023: Dan kudu ne zai gaji Buhari, Osoba
Shugaban kasar 2023: Dan kudu ne zai gaji Buhari, Osoba Hoto: This Day, Femi Adesina - Facebook
Asali: UGC

Ya ce: “Mun kulla yarjejeniya ta fahimta cewa yankin arewa za ta samar da shugaban kasa a lokacin da muka kafa jam’iyyar a 2013. Kuma shugaban jam’iyyar zai fito daga kudu.

KU KARANTA KUMA: Kashe-kashe: Masu siyasar a mutu ko ayi rai ne ke hada kai da yan bindiga don tarwatsa Nigeria, Umahi

“A APC mun samu shugaban kasa tsawon shekaru shida da rabi daga arewa. Shugaban kasar zai shafe tsawon shekaru takwas har zuwa 2023. Shugabancin jam’iyyar ya tashi daga Cif Bisi Akande a kudu maso yamma zuwa ga John Oyegun daga Kudu maso Kudu sannan kuma ya koma ga Adams Oshiomhole, shima daga kudu maso kudu.

“Tabbas, a karshen wa’adin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yarjejeniyar shine cewa Shugaban kasa zai fito daga kudu kuma idan ina maganar kudu, kudu maso kudu, kudu maso gabas da kudu maso yamma na iya samar da shugaban kasa na gaba.

“Don haka, yan kudu maso gabas, kudu maso kudu da kudu maso yamma na iya fito da yan takara don zaben fidda gwanin jam’iyyar kuma duk wanda yayi nasara a zaben fidda gwani na iya zama dan takarar jam’iyyarmu.

“Wannan shine yarjejeniyar da muka kulla a lokacin da muka hade.

KU KARANTA KUMA: PDP ta ce babu wani gwamnan kudu maso gabas a karkashin inuwarta da ke shirin sauya sheka

A wani labarin kuma, Shugabannin yankin Kudu Maso Gabas sun bukaci jam'iyyun APC da PDP su basu tikitin takarar shugabancin ƙasa a 2023.

Shugabannin Ibon sun fitar da wannan sanarwar ne bayan taron da suka gudanar a Abia ranar Talata.

Sun ce lokaci ya yi da ya kamata yankin ta samu damar mulkar kasar kasancewarta ɗaya daga cikin manyan ƙabilu uku na ƙasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng