Tasirin annobar COVID-19 da rufe iyakoki a kan tattalin arzikin Najeriya

Tasirin annobar COVID-19 da rufe iyakoki a kan tattalin arzikin Najeriya

- A shekarar 2020 ne Najeriya ta sake shiga cikin matsijn lambar tattalin arziki

- Coronavirus da cire tallafin man fetur sun taimaka wajen jawo wannan matsi

- Masana suna ganin akwai hannun karancin Dalar Amurka da karyewar Naira

Jaridar The Cable tayi bincike game da yadda annobar COVID-19 da rufe iyakokin kasa da aka yi suka jawo tashin farashi da karancin kudin shiga a 2020.

Alkaluman CPI wanda suke auna sauyin da ake samu a farashin kaya ya tashi sosai a shekarar 2020. NBS mai tattara alkaluma na kasa ta tabbatar da haka.

Tashin farashin kaya da aka rika samu a shekarar da ta wuce ya kara jefa al’umma cikin matsin talauci kamar yadda Ministar kudi, Zainab Ahmed ta bayyana.

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin a rufe duka iyakokin kasa a watan Agustan 2019, da nufin hana shigowar makamai da miyagun kwayoyi cikin Najeriya.

KU KARANTA: COVID-19: An yi wa 'Yan NYSC 35, 000, 731 sun kamu da cuta

A shekarar baran an yi ta fama da hare-hare a gonakin Bayin Allah, wannan ya jawo kayan abinci da masarufi suka kara kudi, farashin kaya su ka zabura a kasuwa.

Masana suna kuma alakanta tsadar kayan abincin da aka samu da karyewar darajar Naira da takunkumi wajen samun kudin kasar waje da tsadar kudin mai.

Cire tallafin man fetur da karin kudin shan wutar lantarki da aka yi a cikin shekarar 2020 ya sake jagwalgwala abubuwa ta yadda harkar kasuwanci ya kara wahala.

Daga cikin abubuwan da suka haddasa matsalar tattalin arziki a Najeriya, akwai annobar nan ta cutar Coronavirus wanda ta addabi mafi yawan kasashen Duniya.

KU KARANTA: PDP ta bayyana shirin da ta ke yi wa Umah tun da ya tsere

Tasirin annobar COVID-19 da rufe iyakoki a kan tattalin arzikin Najeriya
Zainab Ahmed Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Masana tattalin arzikin kasar suna ganin cewa za a cika da fama da wadannan matsaloli a 2021.

Shugaban Kungiyar BAT ya bada tarin dalilansu na goyon bayan takarar babban jagoran jam'iyyar APC a Kudancin Najeriya, Asiwaju Tinubu a zabe mai zuwa na 2023.

Dozie Nwankodu ya ce rashin kabilanci da irin kishin kasar Bola Tinubu ta sa su ke tare da shi.

Kungiyar nan ta Bola Ahmed Tinubu Grassroots Volunteers, ta ce za ta goyi bayan jagoran na jam'iyyar APC muddin ya fito neman takarar kujerar shugaban Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng