Cutar COVID-19 ta harbi Matasa 731 da su ke yi wa kasa hidima a Najeriya

Cutar COVID-19 ta harbi Matasa 731 da su ke yi wa kasa hidima a Najeriya

- PTF ta ce an yi wa masu aikin hidimar kasa na NYSC gwajin COVID-19

- An samu mutum 731 masu dauke da cutar bayan an yi masu gwajin RDT

- Adadin masu Coronavirus a cikin masu NYSC a yanzu ya zarce na baya

Gwajin da aka gudanar a kan mutane 35, 419 da ke bautar kasa watau NYSC a Najeriya ya nuna cewa da yawa sun kamu da ciwon COVID-19.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 6 ga watan Junairu, 2021, cewa daga cikin wadanda aka yi wa gwajin, 730 sun kamu.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19, Boss Mustapha ne ya bayyana haka.

Da yake jawabi a ranar Talata, Mista Boss Mustapha ya ce kwamitin PTF ya yi amfani da gwajin gaggawa na RDT a kan wadanda ake yi wa horo.

KU KARANTA: Coronavirus ta hallaka 'dan Najeriya da ke karatu a Amurka

Sakamakon gwajin da aka gudanar a kan sahu na biyu na masu aikin hidimar kasar (watau Batch B) ya tabbatar da cutar ta yi mugun kamu.

Fiye da 2% na wadanda aka yi wa gwajin sun kamu, wannan adadi ya zarce abin da aka samu a lokacin da aka yi wa ‘yan sahun baya gwajin.

PTF ta ce an samu masu dauke da wannan cuta daga duka sansanonin NYSC da ke Najeriya.

Da yake magana domin bayyana inda aikin su ya kwana, Boss Mustapha ya ce wasu attajirai za su bada gudumuwar na’urar numfashi 100 a Abuja.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun hallaka Bafullatani a Kudancin Kaduna

Cutar COVID-19 ta harbi Matasa 731 da su ke yi wa kasa hidima a Najeriya
SGF Boss Mustapha Hoto: Twitter Daga: @NGRPresident
Asali: Twitter

Shugaban na PTF ya koka game da karancin wadanda ake yi wa gwajin cutar a Najeriya, ya ce duk da akwai dakunan gwaji 100, ba a aikin sosai.

Ku na da labari cewa gwamnatin tarayya ta na cigaba da ƙara ƙaimi domin ganin ta daƙile yaɗuwar cutar COVID-19 da ta ke cigaba da barkewa.

A dalilin haka ne aka hukunta wasu fasinjoji da suka shigo ba tare da sun yi gwajin kwayar cutar ba, an karbe takardunsu, an hana su barin Najeriya.

A halin yanzu abin ya kai ana samun mutane fiye da 1, 000 sun kamu da cutar a rana daya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel