Kwastam ta jaddada hana shigo da shinkafa

Kwastam ta jaddada hana shigo da shinkafa

- Bayan sake bude iyayokin kasa, Kwastan ta jaddada cewa ta hana shigo da shinkafa

- Kwanturola na Kwastam mai kula da Sakkwato da Zamfara ya sake jaddada bude iyakar Illela

- Kwanturolan ya kirayi 'yan kasuwa da su bi dokar shigowa da fitar da kaya daga kasar

Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta jaddada hana shigo da shinkafa.

Abdulhamid Ma’aji, Kwanturola na Hukumar Kwastam ta Najeriya da ke kula da Sakkwato da Zamfara, ya jaddada sake bude kan iyakar Illela a Jihar Sakkwato.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin ta jaddada hakan ne yayin da masu shigo da kayayyaki da masu fitar da kayayyaki a Sakkwato suka yi murna da sake bude iyakar Illela.

Manyan mutane daga Najeriya da Jamhuriyar Nijar sun sake bude iyakar ta Illela.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Zamfara za ta sayi hannun Karin da yakai N250m

Mista Ma’aji ya ce ana sanya ido kan sake bude kan iyakokin don tabbatar da tsafta.

Ya ce rufe iyakokin ya na da fa'ida ga 'yan Nijeriya.

Kwanturolan ya lura da cewa da yawan kayan da masu aikata laifi ke amfani da su an shigo da su kasar ta kan iyakokin kasa ne.

Ya ce ana kokarin shawo kan lamarin.

Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su nuna fahimta da goyon baya ga manufofin gwamnati, sannan ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su bi ka’idojin kasuwanci da ka’idojin kariya.

“Kungiyoyin gwamnati na iya cimma nasara matuka tare da tallafi daga jama’ar kasa da masu ruwa da tsaki wadanda ke taka muhimmiyar rawa,” inji shi.

Kwanturolan ya bukaci masu shigo da kaya da su fitar da su, da tabbatar da bin ka’idoji.

Ibrahim Milgoma, mai fitar da kaya waje ya ce a yayin rufe kan iyakokin, masu fitar da kaya sun bi umarnin gwamnati duk da wahala da aka fuskanta.

Ya ce za su bi ka'idojin da ke kula da sake bude kan iyaka.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya za ta raba wa mata 125,000 tallafin kudi N20,000 - Ministar Jin Kai

Kwastam ta jaddada hana shigo da shinkafa
Kwastam ta jaddada hana shigo da shinkafa Credit: Daily Nigerian
Source: Facebook

Aminu Dan’iya, Shugaban kungiyar Association of Registered Licenced Clearing Agents, ya bayyana cewa akalla kamfanoni 35 ne suka yi rajista a tashar Illela kuma za su bi duk dokokin gwamnati.

A wani labarin daban, Sabon Sakataren din-din-din na Ma’aikatar Gona ta Tarayya, Earnest Afolabi Umakhihe, a jiya, ya yi alkawarin bude kofa ga manufofin samar da abinci cikin sauri, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Bayan ya karbi takaddun mikawa daga Babbar Sakatariya, Hajiya Karima Babaginda, wacce kuma Darakta ce a Ma’aikatar, inda ya bayyana karara cewa batun hadin kai da goyon baya daga daraktoci ba sai an sake jaddadawa ba don cimma manufofi mabanbanta na gwamnatin Buhari a bangaren noma.

Yace: “Na zo nan ne don gudanar da manufofin bayyanannu, koya daga daraktoci, kara daraja, da kuma daidaita al’amuran Ma’aikatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel