2023: Shugabannin Igbo na son APC da PDP su basu tikitin takarar shugaban ƙasa

2023: Shugabannin Igbo na son APC da PDP su basu tikitin takarar shugaban ƙasa

- Shugabannin yankin Kudu Maso Gabas sun bukaci jam'iyyun APC da PDP su basu tikitin takarar shugabancin ƙasa a 2023

- Shugabannin Ibon sun fitar da wannan sanarwar ne bayan taron da suka gudanar a Abia ranar Talata

- Sun ce lokaci ya yi da ya kamata yankin ta samu damar mulkar kasar kasancewarta ɗaya daga cikin manyan ƙabilu uku na ƙasar

Shugabannin ƙabilar Igbo sun nemi manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya biyu su bawa yankin Kudu Maso Gabas tikitin takarar shugaban ƙasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Sun mika wannan bukatar ne cikin sakon bayan taro mai ɗauke da sa hannun tsohon gwamnan Abia, Orji Kalu, da Ike Ekweremadu a ƙarshen taron da suka yi ranar Talata a Camp Neye, Ignore, Jihar Abia.

2023: Shugabannin Igbo na son APC da PDP su basu tikitin takarar shugaban ƙasa
2023: Shugabannin Igbo na son APC da PDP su basu tikitin takarar shugaban ƙasa. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Al'ummar gari sun tsere daga gidajensu a yayinda Boko Haram ta sake kai hari

Sun ce: "Yankin Kudu Maso Gabas a matsayinsa na yanki da ƙabilar Igbo kasancewarsa ɗaya daga cikin manyan ƙabilun ƙasar uku ya cancanci samun shugabancin.

"An kasance ana karɓa-karɓar shugabancin ƙasa tsakanin Arewa da Kudancin Najeriya a yankuna da yawa."

Shugabannin sun ce kansu a haɗe ya ke don ganin yankin ya cigaba kuma basu goyon bayan duk wata kungiya mai neman ɓallewa daga ƙasar.

KU KARANTA: Akwai ƙyakyawar alaƙa tsakani na da Ganduje da Kwankwaso, in ji Shekarau

Kazalika, sun yaba wa shugaba Muhammadu Buhari kan ayyukan gine-gine da ya ke gudanarwa a yankunan kasar biyar.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164