Gwamnatin jahar Zamfara za ta sayi hannun Karin da yakai N250m

Gwamnatin jahar Zamfara za ta sayi hannun Karin da yakai N250m

- Gwamnatin jihar Zamfara za ta zuba hannun jari da haura N250m

- Jihar za ta zuba hannun jarin ne don kara samun kudin shiga na jihar

- Tuni gwamnatin ta amince da sa hannun jarin a sayen wani otal a Abuja

Kamfanin Zuba Jari da Bunkasa Kaddarorin Jihar Zamfara ya ce kamfanin na kan shirye-shiryen sayan hannayen jarin da ya haura Naira miliyan 250 domin bunkasa Harajin Cikin Gida na jihar da samar da karin arziki ga gwamnatin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Manajan Daraktan Kamfanin, Hon. Anas Hamisu Lawal, ya bayyana haka a Gusau, babban birnin jihar.

Ya ce tuni gwamnatin jihar ta amince da fitar da kudin domin nasarar sayen hannun jarin.

Hon. Anas ya kuma kara da cewa nan ba da dadewa ba kamfanin zai fara kasuwancin sufuri da nufin samar da karin guraben ayyukan yi domin bunkasa cibiyar samun kudaden shiga ta jihar.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya za ta raba wa mata 125,000 tallafin kudi N20,000 - Ministar Jin Kai

Gwamnatin jahar Zamfara za ta sayi hannun Karin da yakai N250m
Gwamnatin jahar Zamfara za ta sayi hannun Karin da yakai N250m Credit: The Guardian
Asali: Facebook

Akan kalubalen da ofishinsa ke fuskanta a halin yanzu, ya bayyana cewa rashin isassun ma'aikata na daya daga cikin abubuwan da suka shafi tafiyar da kamfanin, yana mai jaddada cewa an aike da wasika zuwa ofishin Shugaban Ma'aikata kan batun don daukar matakin da ya dace.

Ya yaba da goyon bayan da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Bello Mohammed Matawalle ta baiwa kamfaninsa, musamman ta fuskar sake saka jari don bunkasa ci gaban cibiyar samun kudin shiga ta jihar da kuma samar da ayyukan yi.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi ruwan bama-bamai kan maboyar ‘yan ta’adda a Borno

“Kamar yadda nake magana da ku yanzu, gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Bello Mohammed Matawalle ta sayi mafi kyawun otal a Wuse II da shida na gida mai dakuna uku a Abuja ga kamfanin da nufin bunkasa tsarin saka jari a jihar. da kuma samar da karin kudin shiga ga jihar da kuma samar da karin guraben ayyukan yi ga Matasan jihar mu mai kauna ”. ya bayyana.

A wani labarin daban, Rundunar ‘yan sanda a Zamfara ta kame mutane 18 da ake zargi a kan wani rikici, wanda ya kai ga lalata dukiya ciki har da fadar Sarkin Shinkafi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Muhammad Shehu ya fitar a ranar Lahadi a Gusau.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.