Gwamnan PDP ya jinjinawa shirin gwamnatin tarayya na daukar ayyuka na musamman

Gwamnan PDP ya jinjinawa shirin gwamnatin tarayya na daukar ayyuka na musamman

- Shirin gwamnatin tarayya na daukar ayyuka na musamman ya fara aiki a hukumance

- Wannan shiri ya burge Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta kuma ya bayyana ra’ayinsa game da shi

- Gwamnan ya yaba ma gwamnatin Buhari kan wannan shiri, inda ya kara da cewa al’umman kasar da dama za su ci moriyar abun

Gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa a ranar Talata, 5 ga watan Janairu, ya yaba ma gwamnatin tarayya a kan fara shirin bunkasa ayyuka na musamman a kasar.

Wani jawabi daga gwamnatin jihar Delta wanda Legit.ng ta gani ya bayyana cewa Okowa ya yi jinjinar ne a yayin bikin kaddamar da shirin a yankin kudu maso kudu wanda aka gudanar a Asaba.

KU KARANTA KUMA: Wannan rashin tausayi ne - PDP tayi Alla-wadai da karin farashin wutan lantarki

Gwamnan PDP ya jinjinawa shirin gwamnatin tarayya na daukar ayyuka na musamman
Gwamnan PDP ya jinjinawa shirin gwamnatin tarayya na daukar ayyuka na musamman Hoto: @IAOkowa
Asali: Twitter

Gwamna Okowa wanda ya samu wakilcin kwamishinan labarai na jihar Delta, Mista Charles Aniagwu, ya nuna farin ciki a kan fara shirin inda ya kara da cewa zai taimaka wajen dakile matsalar rashin aikin yi a kasar.

Ya shawarci wadanda suka ci moriyar shirin da su kalli damar a matsayin wani sabon babi a rayuwarsu yayinda yake duba ga karin wasu tsare-tsare makamantan haka don fitar da yan Najeriya da dama daga kangin talauci.

Ya bukaci mutane 25,000 da suka ci moriyar shirin a Delta da su kalli hakan a matsayin wani dama don bunkasa tattalin arzikin jihar da na kasar.

Ya ce:

“Bari na yaba ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya samar da wannan aiki kuma shiri na siyasa saboda yunwa da talauci basu san jam’iyyar siyasa ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Katsina ta ce lallai bata biya kudin fansar sakin daliban Kankara ba

“Idan kuka duba tasirin wannan shiri ta fuskaci tattalin arziki, za ku yaba da gaskiyar cewa a Delta kadai, yan asalin jihar 25,000 ne suke cin moriyar wannan shiri.”

A gefe guda, mun ji cewa an yi watsi da wani rahoto da ke ikirarin cewa wasu gwamnoni daga yankin kudu maso gabas na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar All progressives Congress (APC).

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa babu wani gwamna a karkashin inuwarta daga kudu maso gabas da ke tunanin sauya sheka zuwa kowace jam’iyya.

A cewar jaridar This Day, mataimakin Shugaban jam’iyyar a yankin, Ali Odefa, shine ya bayyana hakan a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Awka, a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel