Wannan rashin tausayi ne - PDP tayi Alla-wadai da karin farashin wutan lantarki

Wannan rashin tausayi ne - PDP tayi Alla-wadai da karin farashin wutan lantarki

- A karo na uku, gwamnatin Buhari tayi karin farashin wutan lantarki

- Wannan karo, gwamnatin ta yi ikirarin cewa ba zai shafi talakawa ba

- Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce wannan rashin hankali ne da rashin tausayi

Jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ta ce rashin tausayi ne gwamnatin tarayya ta yi karin farashin wutan lantarki yayinda kasar ke cikin matsin tattalin arziki.

Jam'iyyar ta bayyana hakan a jawabin da ta saki mai taken, 'PDP ta yi watsi da guzurin sabuwar shekara na karin farashin wutan lantarki,' ranar Talata.

A jawabin, PDP ta ce wannan karin farashin zai tsananta halin da yan Najeriya ke ciki, kuma ta yi kira ga shugaba Muhammasu Buhari yayi gaggawa janye wannan kari.

Wani sashen jawabin yace, "Karin ninki biyu daga N2 zuwa N4 kan kW/hr, kamar yadda hukumar lura ga wutan lantarki kasa ta sanar rashin tausayi ne, rashin hankali ne kuma zai tsananta halin talaucin da yan Najeriya ke ciki wannan lokaci."

"Jam'iyyar ta ce dalilin da NERC ta bayar na wannan kari basu gamsar ba, musamman yanzu da yan Najeriya ke zaton gwamnati zata fito da tsare-tsaren rage illar matsin tattalin arziki."

KU DUBA: Abubuwa masu rikitarwa a kasafin kudin 2021

Wannan rashin tausayi ne - PDP tayi Alla-wadai da karin farashin wutan lantarki
Wannan rashin tausayi ne - PDP tayi Alla-wadai da karin farashin wutan lantarki Hoto: Presidency
Source: Twitter

KU DUBA: SERAP ta ƙalubalanci Gwamnatin Najeriya kan Sowore

Mun kawo muku rahoton cewa hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC, ta karyata rahoton cewa ta kara farashin wutan lantarki na kashi 50 kan abinda kwastamomi ke biya yanzu a fadin tarayya.

NERC a shafinta na Tuwita ta bayyana cewa har yanzu bata bada umurnin kara farashin wuta ba kamar yadda kafafen yada labarai ke watsawa amma unguwannin masu kudi kawai aka karawa.

Hukumar ta ce unguwannin da ke matsayin A, B, C, D da, E aka karawa farashin Kw/hr daga N2.00 zuwa N4.00.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel