'Yar uwata da ta zo min zaman jego ta yi wuff da mijina, Matar aure

'Yar uwata da ta zo min zaman jego ta yi wuff da mijina, Matar aure

- Matar aure ta koka da yadda 'yar uwarta ta yi wuff da mijinta daga zuwa mata zaman jego

- Haihuwa na biyu ne 'yar uwarta ta je zama da ita, saboda mahaifiyarta ta rasu tuni

- Cikin wata daya mijinta ya dirka wa 'yar uwar ciki kuma ya aureta duk da bata so ba

Wata matar aure ta wallafa labarinta mai cike da taba zuciya. Ta bada labarain yadda 'yar uwarta makusanciya ta koma kishiyarta dare daya.

A kokarinta na bai wa wata kwarin guiwar shawo kan matsalar aurenta, ta bada labarin yadda ta yi haihuwa ta biyu amma saboda rashin uwa, sai 'yar uwarta ta je mata zaman jego.

Kamar yadda ta bayyana, bayan isowar 'yar uwarta, sai ta fara wata boyayyar alaka da mijinta.

Babu dadewa kuwa 'yar uwarta ta samu juna biyu kuma mijin ta ne ya dirka mata, The Nation ta wallafa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe dan sandan da ya je ceto wadanda aka yi garkuwa da su a Jigawa

'Yar uwata da ta zo min zaman jego ta yi wuff da mijina, Matar aure
'Yar uwata da ta zo min zaman jego ta yi wuff da mijina, Matar aure. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

Cike da alhini tare da tashin hankali ta dinga rokon 'yar uwarta da ta bar mata mijinta, amma 'yar uwar ta ce bata san wannan ba.

Babu jimawa mijinta ya sanar da ita shirinsa na auren 'yar uwarta, wanda hakan ta faru.

'Yar uwata da ta zo min zaman jego ta yi wuff da mijina, Matar aure
'Yar uwata da ta zo min zaman jego ta yi wuff da mijina, Matar aure. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

Mahaifiyar yara hudu ta ce a halin yanzu tana da 'ya'ya hudu yayin da 'yar uwarta da ta aure mijinta ke da 'ya'ya uku.

KU KARANTA: Da duminsa: FG ta saka sabbin dokokin korona, jerin sunayen wurare 3 da ta rufe

A wani labari na daban, fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Maryam Booth, ta tabbata a gwarzuwar jarumar Africa Movie Academy Awards, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Maryan Booth ta samu nasarar ne sakamakon rawan da ta taka a wani fim mai suna The Milkmaid, inda ta bige Chairmaine Mujeri (Mirage), Linda Ejiofor (4th Republic) da wasu mutane hudu.

A cike da murnar wannan nasarar, jarumar ta wallafa rubutu a shafinta na Instagram kamar haka: "Ina taya kaina da iyalan fim din milkmaid murna. Muna fatan karin nasarori, sai mun hadu nan gaba a Oscar."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel