Iyaye sun daina aurar da ‘ya’yansu mata a Kano saboda dokar kayyade sakadin aure

Iyaye sun daina aurar da ‘ya’yansu mata a Kano saboda dokar kayyade sakadin aure

Ana can an yi jugum jugum a wani kauye mai suna Kera dake cikin jahar Kano, inda mahukunta a kauyen suka sanya dokar kayyade kudin aure da nufin saukaka ma samari da masu neman aure, amma sai hakan ya janyo ma matan tsangwama.

BBC Hausa ta ruwaito a dalilin wannan doka an kwashe watanni hudu ba’a daura auren ko mutum daya a kauyen Kera ba, sakamakon rashin amincewa da dokar da iyayen yan mata suka nuna.

KU KARANTA: Uwargida ta shigar da karar Maigida saboda yana yi ma kananan yara fyade a Kaduna

Dagacin wannan kauye mai suna Ado Sa’id ya gindaya N137,000 a matsayin kudin aure wanda ake son duk wani manemin aure a kauyen zai biya, amma iyaye sun ce ba zata sabu ba, saboda hakan tamkar wulakanta musu yara ne.

A cewar dagacin, wannan kudi N137,000 shi ne zai maye gurbin kudaden da ake kashewa a al’adance wajen neman aure kamar su kudin lefe, kayan daki, akwati, kayan kichin da dai sauran kudade da namiji ke kashewa.

Don haka dagaci Ado yake ganin wannan matakin ya fi sauki, kuma zai sa aure ya yi sauki a kauyen, bugu da kari ma, dagacin yace ba shi kadai ya yanke shawarar kaddamar da wannan doka ba, sai da ya tattauna da iyayen yara a kauyen.

Wata mata a garin ta bayyana bacin ranta da wannan doka kamar haka; “Muna da ‘ya’ya mata, amma an mayar dasu gwanjo, an hana samari su neme su su yi musu abin duniya, kudin aure N137,000 ne zai yi ma yarinya kayan kicin, kayan kwalliya da zannuwa?”

Shi ma wani uba mai suna Sani Kera y ace yana da yara biyar da suka isa aure, kuma suna da shirin aurar dasu, amma wannan doka ta sanya sun dakatar da batun auren sai baba ta ji.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan kasar Bangladesh ta kama wani mutumi dan shekara 45 mai suna Abu Baker sakamakon kararsa da matarsa ta shigar gaban Yansanda inda take zarginsa da aure sau 60 a cikin shekaru 25.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel