Yadda kayan lefe ke hana aure a kasar hausa

Yadda kayan lefe ke hana aure a kasar hausa

Da yawa daga cikin mazaje hada kayan lefe shi ke hana su yin aure a kasar hausa saboda tsabar kudi da a ke kashewa wajen hada kayan sanadiyar zamananci da al'adu irin na bahaushe

Kamar yadda a ka sani a kasar hausa, daya daga cikin batutuwan da suke tasowa wajen yin aure shine kayan lefe da namiji zai hadawa wadda ya ke neman auren ta.

Shi dai wannan lefe kamar yadda kowa ya sani al'adar ce ta kawo shi kuma hada kayan lefe ya na bukatar kashe kudi musamman idan aka yi duba da zamananci da kuma gidan da macen da za a aura ta fito.

Hada kayan lefe ga namiji akwai kashe kudi ko daga ina kuwa amaryar ta sa ta fito walau gidan Malam Shehu ko Alhaji Shehu, wanda wannan abu shike korar mazaje da dama daga yin aure.

Yadda kayan lefe ke hana aure a kasar hausa
Yadda kayan lefe ke hana aure a kasar hausa

Da yawa daga cikin mazaje za su so su burge matan da za su aura don duk macen da aka ce an kawo wa lefe za a fara tambaya a cikin dangi da kawaye shin kaya kala nawa aka sanya mata cikin akwatin ta na lefe da kuma tsadar kayan.

Wannan al'amari ya zama ruwan dare a kasar hausa ta yadda burin ko wace mace a ce ai mijin da za ta aura ya gwangwaje ta wajen kayan lefe saboda a samu a bin magana cikin kawaye da dangi.

KU KARANTA: An dakatar da wasu mata 3 maniyyata aikin hajji a jihar Kwara

Shi kuwa wannan kayan lefe ba kananun kudi a ke kashe wa ba wajen hada shi don haka wasu mazajen ga shi su na da bukatar yin auren amma idan su ka tuna da kayan lefe sai su yi ragas.

Sanadiyar wannan abu ne wasu mazajen ke kafa kungiyoyi ma su sunan "ba za mu yi aure ba sai an soke lefe" a cikin jihohin mu na arewacin Najeriya.

Sai dai shi aure idan mutum ya biye ta abinda zai kashe to kuwa da yawa ba za su yi auren ba don ko su iyeyen yariya su na kashe makudan kudi wajen yi ma ta kayan daki.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel